Main menu

Pages

AMFANIN BIYAR DA RUWAN KUKUMBA KEYI GA LAFIYAR DAN ADAM

 



Yadda za ayi amfani da Ruwan Kokumba wajen magance abubuwa guda biyar.

Masana kiwon lafiya sun bayyana nau’ukan amfanin ruwan kokumba a jikin dan’adam. Ruwan kokumba ya zama sanannen ruwan sha ga masu son gyaran jiki, amma ba hakan yake ba a wajen gama garin mutane sanadiyar rashin sanin fa’idar ruwan wajen kiwon lafiya managarciya. Ga kadan daga cikin hanyoyi da ruwan kokumba zai amfani jikin Dan’adam. 




1 - Yalwar ruwa a jikin Dana’dam: 

Ruwa wani muhimmin jigo ne wajen gudanar da al’amuran jikin Dan’adam, ta yadda idan babu ruwa a jikin mutum zai tagayyara ya lalace. 

Adadin ruwa da ya kamata a ce mutum ya sha a kullum ya na danganta ne da yanayin jiki zuwa jiki. 




Kofi shida zuwa takwas na ruwan kokumba zai samar da wadatacciyar lafiya a jikin Dan’adam, duk da sanin cewa ruwa wani abu ne da yake gundurar mutum da zarar ya koshi, amma ruwan kokumba zai sanya mutum ya yi ta neman karin abinci, saboda dandanon shi da ya banbanta da na ruwa. 




2- Hana nauyin jiki: Ga duk wani mai son rage nauyin jikinsa, to ya dunga yin amfani da ruwan kokumba ya na matukar taimakawa wajen inganta hanyoyin narkar da maiko a jikin Dan’adam. 




Sau tari mutum zai rasa gane cewa yunwa yake ji ko kuma kishi, ta yadda mutum zai gane haka shi ne, ya samu kofi daya na ruwan kokwamba mai sanyi ya fara sha, idan yunwar ta gushe, to daman kishirwa ce kawai, amma idan yunwar ba ta gushe ba to lallai mutum zai gane cewar yunwa ce ke damun sa kuma sai ya nemi abinci.



3 - Hana yaduwar cutar daji (kansa): Kokumba tana taimakawa wajen hana kamuwa da cutar daji sanadiyar sunadaran ‘cucurbitacins’ da ‘lignans’ wadanda suke hana kamuwa da cutar kansa wanda wasu ke kiran ta da suna cutar daji. 

Amfani da ruwan kokumba yana rage yaduwar cutar kansa da take kama ‘ya’yan maraina na mazakutar namiji. 




4 - Rage hawan jini: Yin amfani mai yawa da gishiri wanda yake kunshe da sinadarin ‘sodium’, yana assasa gamuwa da cutar hawan jini. Ita kuwa kokumba tana dauke da sinadarin ‘potassium’ wanda yake wanko duk wani sinadarin na ‘sodium’ daga cikin kodar mutum, wadda daman ita ce mai rarraba amfani na duk wani nau’in abinci da mutum ya ci. 




Saboda haka, shan ruwan kokumba yana kara sunadarin ‘potassium’ a jikin Dana’dam wanda yake taimakawa wajen hana samun cutar hawan jini. 




5 - Gyaran fata: Ruwan kokumba yana sanya fata ta yi kyau fyas-fyas, domin ga mai shan ruwan kokumba ko da yaushe jikinsa zai zama cikin wadaceccen ruwa don daman bushewar fata ita ke sanya fatar Dan’adam ta lalace. 



Ruwan kokwamba yana hankado duk wani dafi ko gubar da take jikin fatar Dan’adam kuma kokumba tana da sinadarin’bitamin B-5′ wanda ya ke magance kurajen fuska. 




Domin haka, sai mu dage da shan ruwan kokwamba domin samun cikakken lafiya yadda ya kamata.

 Allah ya ba mu ikon yin amfani da wannan dama ta shan ruwan kokwamba.

Comments