Main menu

Pages

YADDA AKE SON MAI CIKI TA YAWAITA CIN DABINO DAGA BAKIN LIKITA

 



Amfanin Dabino ga Mata Masu juna biyu wajen magance doguwar nakuda daga Bakin kwararriyar Likita.


Mai karatu barka da wannan lokaci, a yau za mu kawo ma, amfanin dabino ga lafiyar mata ma su juna biyu, ko mu ce amfanin dabino wajen saukakawa mata ma su ciki nakuda.




Kuma ga ma su biye da wannan shaf, tuni mun gabatar da wata makala mai taken "Amfanin Dabino Ga Lafiyar Dan-adam".




A irin binciken da wannan shafi ke yi domin zakulo mu ku abubuwa ma su amfani ga lafiyarmu, mun samu nasarar dora hanunmu kan sakamakon wani bincike da wata kwararriyar likita a fanni abinci mai gina jiki da ke aiki da wani kamfani mai zaman kansa, dake da hedikwatarsa a birnin ikko, ta fitar dangane da amfanin dabino ga mata ma su juna biyu. 




Likitar mai suna, uwargida Jane Eleodi, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, amfanin dabino ga lafiyamu, musamman ga 'yan uwa mata ma su ciki.




Ta yi tsokaci kan irin sanadaran inganta lafiya da dabinon ke kunshe da su, sannan ta kawo sakamakon bincike har guda uku da aka gudanar kan mata ma su juna biyu da su ka ci dabino, sannan aka kwatanta su da matan ma su ciki da ba su ci dabinon ba.




Ba tare da bata lokaci ba, zai yi kyau mu bar ku da wannan likata don ji daga gare ta, amfanin dabino ga lafiyar dan-adam, musamman mata ma su ciki, don kuwa waka a bakin mai ita ta fi dadi. Da fatan a sha karatu lafiya.




Kwararriyar likitar a fannin abinci mai gina jiki, Uwar-gida Jane Eleodi, ta shawarci mata masu juna biyu da yawan cin dabino, musamman ma a makwannin karshe-karshe kafin lokacin da za su haihu.




Ta ce, yawan cin dabino na samar wa matan sanadaran gina jiki, sannan kuma ya rage mu su doguwar nakuda.




Eleodi, wacce kwararriyar likita ce a fannin abinci mai gina jiki da ke aiki da wani kamfani mai suna 'JSPRINGS Nutrition and Health, Support LTD, da ke jihar Legas, ta ba da wannan shawara ne yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar wannan Alhamis.




Uwar-gida Jane ta ce, "An gudanar da zuzzurfan bincike kan dabino, kuma an gano ya na taimakawa mata ma su juna biyu wajen magance mu su doguwar nakuda.




"Cin dabino a makwannin ƙarshe kafin haihuwa na samarwa mata ma su ciki sanadaran inganta lafiya, sannan ya hana mu su dadewa a kan gwiwa.




"Cin dabino tun daga farkon ciki zuwa haihuwa na taimakawa mata ma su ciki wajen samarwa jikinsu sanadarai ma su gina jiki kamar, nau'ikan bitamin daban-daban, da kuma 'minerals' wadanda kuma ke taimakawa wajen girman dan tayi. Bugu da kari kuma su na da matukar muhimmanci ga lafiyar mahaifiyar.




Hakanan ta kara da cewa, "Ana samun muhimman sanadarai ma su dinbim yawa cikin dabino, da su ka hada da, Vitamin A, E, K, C, Thiamin, Riboflavin, Folates, Niacin, B6, Pantothenic acid, Zinc, Calcium, Iron, Choline, Magnesium, Phosphorus, Potassium, Manganese da dai sauransu.




"Sauran sanadiran gina jiki da ke kunshe cikin dabino sun haɗa da Omega3 fatty acid, Betaine da 'copper', '' in ji ta.




Eleodi ta kuma ce, 'ya'yan itaciyar sun ƙunshi sanadarin 'Tannins', waɗanda aka tabbatar su na taimakawa mata ma su juna biyu kwarai da gaske.




Ta ce, dabino ya kasance tushen samun sanadaran 'natural suger da kuma clories' waɗanda ke taimakawa mata ma su juna biyu su samu karfi lokacin nakuda.




Kwararriyar likitar ta ce, kodayake, binciken baya-bayan nan ya nuna cin dabino na taimakawa wajen saukin nakuda da kuma hana doguwar nakudar, amma akwai buƙatar karin bincike da nazari da za su marawa wannan sakamako baya, sannan da gano wadansu tasirin na dabino.




Ta ci gaba da cewa, wani bincike da aka gudanar kan wasu mata 69 da suka ci kwayar dabino 6 a kowace rana har tsawon makonni 4 kafin kwanakin da za su haihu, ya nuna cewa sun samu kashi 20 cikin 100 na saukin nakuda, da kuma fara nakudar ba tare da an taimaka mu su ba, sabanin 'yan uwansu da ba su ci dabinon ba.




Sannan nakudarsu, ta kasance gajeriya idan aka kwatanta ta da ta 'yan uwansu da ba su ci dabinon ba, a tsawon wadannan kwanaki.

Comments