Main menu

Pages

SUFFOFI BIYAR DA MACE TA GARI TA KEBANTA DASU WAJEN MIJINTA




Suffofin Kamillalliyar Mace ta gari ta kirki guda biyar da in tana dasu to ita din Mace tagari ce wajen Mijinta.


Mace ta gari tanada suffofi guda biyar sai ki duba ki gani shin kina da wadannan suffofin, ko kina da wasu baki da wasu sai ki gyara. Gasu kamar haka;.



1. Itace wacce idan mijinta ya kalleta zaiji dadi aransa, wato zaiyi farin ciki duk saddaya kalleta, 

Abubuwan da sukesa miji ya kalli matarsa yaji dadi kuma guda hudune,



A. Suyi Auren Soyayya wato ya zamana cewa yana sonta, Matukar bai sonta duk abunda zatayi bazata burgeshiba,



B. Taji tausayinsa wato ta rika nuna masa cewa tana tausayinsa kuma ya fahimci hakan, duk yada namiji yakeson mace idan ya gano bata tausayinsa wlh zai tsaneta kuma zai rika boye mata sirrinsa,



C. Ta kware afagen kwalliya da tsafta da iya Soyayya, duk sonda yake maki idan kika zama kazama zai tsaneki kuma wasu matan zasu rika dauke masa hankali awaje, 



D. Kyau, maza suna son mace mai kyau duk sadda suka kalleta sunajin dadi sosai aransu, 


(Ki kula da wani abu Anan, yadda kikaga na jero makisu haka, to haka suke guda na biwa guda)



2. Sufar mace ta kwarai ta biyu itace idan ya Umarceta tayi zatayi, bata Saba masa sai cikin abunda Allah ya hana,



3. Idan ya hanata zata hanu, bazatayi abunda baya soba, 



4. Baya zarginta da Zina ta zama kamilalliyar mace mai tsoron Allah,



5. Baya jin tsoronta game da Dukiyarsa, bata mai sata idan baya nan zata kulamai da Dukiyarsa bata kumayi masa almubazzaranci da abinci ko makamancin haka,


Kiyiwa kanki hisabi!

Comments