Main menu

Pages

HANYA MAFI SAUKI DA ZAKI BI DON HADA CUP CAKE

 Yanda akeyin hadin Cup cake a habya mafi sauki.


Abubuwan da za a bukata wajen hadawa;

- Flour rabin loka/mudu

- Butter simas 2

- Kwai 15

- Sugar gwangwani 2

- Baking powder cokali daya table spoon

- Flavor quater tea spoon.Yadda za a hada:

Ki sami kwano ko roba ki zuba Butter dinnan duka sai ki zuba Sugar, ki juya su ki yi ta buga shi domin Sugar din ya narke. Daga nan sai ki zuba kwai ki yi ta buga shi sosai,Idan kina da Mixer ma zai fi haduwa sosai. Sai ki zuba flour da baking powder da flavor ki yita bugawa, har sai kin ga ya hade. Wasu kuma suna zuba flavor da baking powder a flour kafin su juye.Sai ki sami murfi ki rufe, ki je ki kunna oven, idan gwangwanin cake kike dashi sai ki shafa Butter ko Mai, idan kuma cup cake kike dashi to sai ki zuba kwabin ki sa a Oven ki gasa.Note: Flavor na gari zaki yi amfani dashi, sannan idan kika cika domin kiyi gwaninta toh zayyi caccaki a saman cake din.Sannan Baking Powder din na gwangwani zaki yi amfani dashi, ba na roba ba, domin shine zai sa ya tashi sosai.Wannan shine hanya mafi sauki na yin cake. Ki gwada dan kadan zaki ga canji. Ko baki sa milk ba zai yi dadi.


Idan zaki yi dan kadan kuma ga yawan da zaki sa abubuwa saboda kada ki yi dayawa yazo bai yi kyau ba ki yi asaran kaya

Comments