Main menu

Pages

AMFANIN YAWAITA SHAN ISASSHEN RUWA GA JIKIN MACE

 



Amfanin yawaita Shan ruwa ga jikin Mace da illar da rashin Shan isasshen Ruwa ke haifarwa


Shan ruwa isasshe yana gyara al'auran mace. Kuma ya rinƙa gyara yanda ƙamshin sa ko ɗanɗanon sa ya ke ga mai shan ruwa sosai. Shan ruwa mai kyau mai yawa yana flushing system ɗinki, kuma ya iya fitar da infections tare ma da wasu cutuka ko wari. Rashin shan ruwa isasshe zai iya haddasa miki abubuwa da yawa a jikinki kamar:


- Yawan kasala da gajiya da yawan bacci, ciwon kai, jiri, jin amai, ko jin zazzabi


- Matsewar bayan gida.


- Ciwon gaɓoɓɓi ko na jijiyoyi.


- Lalacewar fata ko ido dss.


Waɗannan ƙananan matsaloli kenan. In kina shan ruwa isasshe ko da futsarin ki yellow ne, ranar ko washe gari zaki ga ya koma fari qal. Don haka mata mu rinƙa ƙoƙarin shan ruwa musamman kofi ɗaya na safen nan kafin a ci komai.


Comments