Main menu

Pages

ABUBUWAN DAKE QARA INGANTA ZAMAN AURE YAYI DADI DA QARKO

 Abubuwan dake Kara Inganta zaman Aure, yayi dadi da Karqo

Kamar yadda Al'kurani ya karantar damu; abinda ke karawa aure inganci yai danko ya zauna shine: (ASHURU HUNNA BIL MA'ARUF) Ashiru hunna bil ma'aruf.... Anason Namiji ko yaushe ya zama kwasai-kwasai kamar goron bakin sarki. Namiji kwas-kwas yai shar cikin tsafta, da ado. Bawai arika ganinsa Bargajaja ba.
Sannan Namiji ya zamto yana wanka, duk wani guri ajikinsa da yake da loko da gashi yake fitowa toh ya zama yana kawarwa, yana askewa ya gyara farcensa, ya goge kafarsa da sanya sutura mai kyau.
Sannan Namiji ya rika amfani da turare, sannan bakinsa ya rika asuwaki ko brush akai akai. Abinda ya shafi su albasa ko Tafarnuwa ka kiyayi cinsu saboda MU'AMALARKA da kusaci da zakayi da mai dakinka. Anaso Maigida ya kiyaye wannan.
Sannan kullum Asuba anaso ka jaddada niyyar zaka rike Matarka tsakani da Allah, kuma zakai Hakuri da ita.
Idan ya zamto kana ado kana gyara jikinka, kana kwalliya, gami da kamshi komi na tafiya daidai. Toh abu na gaba shine kiyaye harshenka
Ka kiyaye harshenka, ka rika fadar kalmomi masu kyau, ka dinga samo suna wanda zai yima Matarka dadi ka ringa gaya mata. Domin inka duba kissar Nana Aisha da Annabi (SAW) aikaga wani irin suna yake fadamata. Tarhimi yake mata sai yace: YAA AH'ISHUUU. Tana jindadin baice mata Aisha ba, sai A'eishuuu
Tanajin dadin cewa wanda yafi kowa kaunarta aduniya shi yake fadamata wannan kalmar.Alaihis salam wassalat. Don haka kasa mata suna mai kyau.
Sannan lokacin da zakasata yi maka wata hidima. karka sata da zummar gadara, da iko irin dole tayi dinnan, A'ah, ba'a haka


Da lumana ake sa Mace aiki. Misali; wance.... atashi ayi kaza da kaza badon sa aiki ba. Ita kuma inta tashi sai kaji tace; Ai ka isane.

Sai kace; A'ah wane ni ni, kurum nafadane badon sa aiki ba. Ina ni ina wannan. shikenan sai kaga ta tashi cikin nishadi. Haka akeyi yan uwana Maza. Da Raha da komai, anayi ana wadangarci haka akeso, kaita samata farin ciki azuciyarta harta dinga jin Gidan Auren yafi Gidan da aka haifeta.
Daga sanda Matar mutum tafijin dadin gidansa akan gidan mahaifatan toh daga lokacin Mutum ya zama KARIMI. Ka kar6ota "BI AMANATULLAHI WASA'ALATU FARJIHA BI KALIMATULLAHI...." toh yi kokari ka kula da ita.Sannan duk abunda zai kuntata mata toh yi kokari ka farantamata. Koda wani abunne can daban da bakaine sanadin 6acin ranta ba.
■ Bazai yiwu kanaso kaga matarka fes-fes ba amma kai kace bazakai tsafta ba. Itama haushi takeji taga ka ware wata riga ko jallabiya kullum da ita kake zaune mata agida. Addinin mu bai barmu a duhu ba. 

Wajibi ne mui tsafta domin cikon addini ce.


Allah Yasa mudace da dukkan Alkhairi 

Comments