Main menu

Pages

ABUBUWAN DA YA KAMATA MATAN AURE NAYI DON HANA MAZANSU YAWON DARE

 Abubuwan da ya kamata Uwargida da Amarya tana ma Mijinta don Hana shi fita yawon dare.

Mu Lura da wannan 'yan'uwa na mata, hiran dare nasa mai-gida ya daina fita yawo da daddare, saboda baya samun hirar dare daga gareki, kuma galibi idan suka fita, sai sun raba dare ana tadi a waje, lokacin da zai dawo, ke kuma sannan kin yi barci, kinga irin wannan ina amfaninsa.
Ki dinga jawo hankalin mai-gidan ki, ta wannan sigar, domin ya kaucewa hanyar banza kamar Zina, ya debo cuta, shan giya da sauransu.
A kullum bayan sallah isha'i idan akaci abinci, sai a dasa Hira, har lokacin barci yayi, in ma mijinki baya so, to yau da kullum idan ya ga kina yawan damunsa da hirar to zaki ga ya dawo yana so, muddin ki ka saba masa da wannan, ba zai dinga fita yawo ba amma idan kika yi sakaci ya Saba da fita, to duk randa kika so ya bari ba zai bari ba.
Sakacin wasu Matan na barin masu aiki na girka abinda Mijinsu zai ci.

Wannan babbar matsala ce, musamman ga matan masu kudi da kuma mata masu aikin gwamnati da matan sarauta.Ma'ana anan shine sai kaga mace ta zauna ta mike kafa a gida ba zata tashi ta yima mijinta girki ba. Koda kuwa yayi tafiya ne ya dawo, sai dai ta sa mai aikinta.

   


Duk mai wannan halin gara ma tun wuri ta daina, ko kuma ki sakar ma mai aiki ragamar gidanki, kama daga

☆ Abinci 

☆ Kula da yara

☆ Aikin gida 

*  Gyaran dakin ki Dana mijinki.


Ko kuma idan mai-gida yasa ki aiki, kice ma mai aikin ta tashi tayi!


Sai kace ita ya ajiye, ba ke ba, ya kasance idan ba wurin kwanciya ke babu wani abu da Zaki iya masa komai sai (HOUSE GIRL) wannan kuskure ne babba._Muddin kika zauna, sai ta zauna miki domin kina da tashin hankali a gabanki, saboda ko mai aiki bata nuna tana son sa ba, shi zai iya nuna yana sonta, ko ya Fara tunanin Kara aure, don haka kar ki bada ragamar dawainiyar mijinki da me aiki, mu gyara wannan halin namu.

                            


Comments