Main menu

Pages

ABUBUWA BIYAR DA YA KAMATA A RAGE CIN SU A CIKIN ABINCI

 Abubuwa guda biyar dake ci cikin abinci ko abinsha dake haifar da ciwon Hanta.

Hanta dai wata tsokace mai matukar amfani, ta na taimakawa Dan Adam wajen lalata wasu kwayoyin jini da suka lalace.Ana samun hanta ne a cikin Dan Adam. Hanta dai wata aba ce mai matukar anfani a cikin jikin Dan Adam ake samu a cikin ciki.Ko shakka babu hanta mai lafiya kusan dai-dai take da mutum mai lafiya haka zalika hanta marar lafiya ma dai-dai take da mutum marar lafiya.
1- Abinci Mai kitse.

Dukkan dange-dangen abinciccika masu kitse na da matukar hadari da lafiyar hantar dan adam, Abincin da ke da kitse yakan ba hanta wahala sosai kasantuwar ita ce ke kula da sarrafa dukkan abin da ke shiga cikin dan adam, Yawan cin kitse kan cutar da ita sosai.
2- Sugar

Kadan daga cikin ayyukan hanta shine sarrafa suga zuwa sinadarin kitse kuma kamar yadda muka karanta a sama, yawan hakan ma kansa yana da lahani ga lafiyar hantar.
3- Gishiri. 

Binchiken masana ya nuna cewa abinci mai gishiri kan yi lahani ga jiki musamman ma dai kasantuwar hanta ita ce ke da alhakin sarrafa sinadarin, Yawan gishiri kan wahalar da hanta ya sanya mata cuta.
4- Barasa

Shan giya ma dai kan taimaka wajen lalata hantar dan adam kasantuwar cewa takan wahalar da hantar wajen sarrafa ta.
5. Abincin cikin Gwangwani.

 Kasantuwar yawancin wadannan abinciccikan nan na dauke da gishiri da suga mai tarin yawa, hakan kuma na matukar wahalar da hanta wajen sarrafawa.
Don haka sai a kiyaye cimaka irin wadannan, wasu sinadaran Kuma ana Amfani dasu dai dai misali kar a cika, kamar sugar da Gishiri.

Comments