Yadda Ake amfani da Qaro wajen magance ciwon Qoda da irin Qarin da za ayi amfani dashi
A Cikin Sassan Dan Adam cutar koda a wannan zamanin ta zama ruwan dare, saboda Allah kadai yasan yawan mutane da ta yi sanadiyyar ajalinsu, saboda haka ‘yan uwa kuzo mu taimaka mu ceci rayuka daga halaka daga wannan mummunar cuta.
A jaridar UKAZ da ke garin Palastine an rawaito cewa wani saurayi mai shekaru 35 ya warke daga cutar koda bayan an yi masa wankin koda (dialysis ) na tsawon shekara daya abun bayyi ba, sai sanadiyyar amfani da “Qaro”. Likitan ya tabbatar masa da cewa ya warke har abada kuma baya bukatar wankin koda nan gaba.
Sannan har yanzu an samu wata yarinya mai shekaru ashirin da daya 21 wacce ta samu wannan matsalar ta koda, aka je aka yi mata gwaji a asibiti, Creatinine nata ya hau zuwa 550 amma sai ya ragu ya koma 200 bayan ta yi amfani da karo na tsawon sati uku kacal.
Misalai irin wannan suna da yawa saboda haka ya zama dole ‘yan uwa su yada wannan bayani saboda kowa ya karu.
To ya ya za a yi amfani da shi?
Za a nika karon ko a daka sosai har ya yi laushi, daga bisani sai a debi cikin babban cokali biyu da safe a zuba a ruwa kofi daya, sai a barshi kamar sa’a biyu ko uku har ya narke, sai a garwaya sosai a sha da safe kafin, sannan a maimaita haka da yamma sai asha kafin bacci.
Kalar Qarin da zakuyi amfani dashi:
Za ku samu asalin karo na itacen karo wato (Kolkol) da shi ake yin amfani.
Haka za a cigaba da amfani da shi har a samu sauki domin karo bashi da wata illa kamar sauran magunguna.
Allah Ya Sa Adace Ameen.
Comments
Post a Comment