Main menu

Pages

YANDA ZA AYI AMFANI DA GANYEN GUAVA DA RUWAN ALBASA A GASHI

 Yanda za ayi amfani da Ganyen Guava da Ruwan Albasa wajen Hana karairayewar gashi da Kara masa tsawo.

A maimakon badda makudan kudade wajen sayen mayukan kara gashi da hana zubewar shi, za a iya amfani da ganyen gwava wanda bincike ya nuna cewa ya fi karfi da inganci akan yawancin kayan gyaran gashin da ake sayarwa na kamfani . 
Ganyen gwava na dauke da sinadaran da ke kara yawan gashi, ya tsaida zubar shi, ya kuma kara mashi lafiya da sheki . Ga yadda ake amfani da shi : Za a dafa ganyen gwava kamar cikin hannu ko damka daya a cikin lita daya na ruwa, sai a barshi ya tafasa na tsawon minti 20, sannan sai a sauke a barshi ya huce . Idan ya huce za a matse ganyen a tace ruwan . 

Wannan ruwa shi za a mursuka cikin gashin tundaga kasa Ko dai a mursuka ruwan bayan an wanke gashi a barshi na tsawon awanni sannan a wanke, ko kuma a mursuka shi da daddare, a rufe da hular leda a kwana da shi . 
Idan aka ci gaba da amfani da Ganyen gwava, za a ga banbanci . 

Gashi zai kara laushi, ya karfafa , sannan ya daina zuba, al ’amarin da zai sa shi ya kara tsawo cikin dan kankanin lokaci Insha Allah.


Amfanin Ruwan Albasa wajen gyaran Gashi

Yin amfani da ruwan albasa yana matukar taimakawa wajen inganta koshin lafiyar gashi, tare da yaye wasu cututtukan gashi da kai ya bayyana a gashin. Ga jerin amfani 5 na ruwan albasa wajen inganta koshin lafiyar gashi. 1. Amfani wajen inganta koshin lafiya da yalwa tare da habaka fitowar gashi, sanadiyar taimakon sunadarin enzyme mai tallafawa wajen narkewar kwayoyin hydrogen peroxide masu inganta lafiyar gashi. 2. Yana taimakawa wajen inganta kwayoyin follicle na cikin gashi wadanda suke kunshe da sunadarin Sulfur. Matsayin Sulfur tamkar taki ne a gona, ya na kuma hana sirancewar gashi da hana karyewar su.3. Sunadaran antioxidants suna tallafawa wajen hana fitowar furfurar gashi da wuri. 


4. A sakamakon sunadaran antibacterial na cikin ruwan albasa, su na taimakawa jijiyoyin gashi wajen kubuta daga cututtuka musamman amosani tare da inganta koshin lafiyar su.


5. Yana kuma inganta zagayawan jini a kafofin gashi.

Allah Ya sa a dace.

Comments