Main menu

Pages

AYYUKAN DA YA KAMATA MACE TA KAURACEWA LOKACIN AL'ADAH
Yadda ya kamata Mace ta kula da kanta lokacin Al'adah da ayyuka da bai kamata yanayi ba

lokacin al'ada lokaci ne da mace zata tsaya ta kula ta ga cewa bata sakin jikinta kamar lokuta da bata al'ada ba, musamman ma budurwa wacce bata taba aure ba, har itama matar auren wacce ta San ciwon kanta, kuma bata son taga miji yayi watsi da ita da wuri ko yana tunanin Karin aure da wuri. 
To sai ki tsaya ki maida hankali wajen kulawa da jikinki a lokacin al'ada da kuma haihuwa, saboda itace mace a duk lokacin da take cikin al'ada to a wannan lokacin jikinta budewa yake yi, shi yasa idan mace na cikin al'ada idan akwai manya a kusa, sai su rinka hanata daukan abu mai nauyi

Bokiti da kuma tsalle-tsalle ko kazar-kazar saboda wannan lokacin jikinta a bude yake.

Idan ko tana wannan kazar-kazar din to dukkanin jikinta budewa yake yi.
Don haka idan budurwa tayi aure kuma ta kasance mai irin wannan dabi'a shine sai ki ga an sami matsala da miji yana zarginta da ko tana yawan banza tunda bai same ta a matsayin wacce bata taba aure ba.

Nan kuwa ba haka bane, yawan tsalle-tsalle ne ya jawo a ya yin al'ada.
Idan kuma matar aure ce to sai kaga jikinta ya sake budewa, idan ta gama al'ada ta koma turaka sai ki samu maigida bai damu da ya rika waiwayarta ba saboda a madadin jikinta ya matse a a sai ma ya Kara budewa da yayi.

Ki kula da irin zaman da Zaki yi da tafiya ki kuma kiyaye da daukan abu mai nauyi.


Ya zama dole ki yawaita yin wanka karancin sau biyu a rana, safe da yamma.


Sannan wanka da sabulun mai kamshi da kuma ruwan dumi, sai kuma ki shafa mai mai kamshi ki saka turare mai kamshi sannan a koda yaushe ki rinka yawan canja pad din da ke jikinki saboda shi jini ya danganta, wani yana karni wani babu wani ma wari yake, don haka yana da kyau a tsaftace jiki.
Saikuma amfani da miski lokacin da zaa sa pad, shima kuma yana taimakawa sosai wajen rage karni ko warin jinin al'adah, sai kuma a yawaita shan ruwa sosai da kuma tsarki da ruwan dumi.

Comments