Main menu

Pages

YADDA ZAKI HADA TSUMI HADIN DABINO DA NONON RAKUMI

 Yadda Ake Hada Tsumin Amarya na Dabino da Nonon Rakumi

 Wata fa'ida ce wacce ya kamata kafin na fada kowacce mace da zata ya amfani da ita ta bani wani tukwici amma saboda maigida na bar muku shi kyauta.
Macen dake so ta rikita maigida to ga hanya mai sauki, ke ko mota kike so indai kikai wannan hadi tofa kin samu, amma fa idan an samu mota kar a manta dani.


Zaki nemi wadannan abubuwan;

1. Dabino

2. Kwakwa (coconut)

3. Nonon Rakumi

4. Zuma.Yadda za a hada

Da farko zaki cire kwallon dake cikin dabino, sai ki kawo kwakwar ki bayan kin bare bawon ta ki samu ruwa kadan ki zuba a kai kiyi blending nasu bayan kin gama sai ki kawo zuma kamar rabin kofi nonon Rakumi kamar kofi daya ki hada da kwakwar nan da kika hada da dabino ki hade da zuma da nonon Rakumin waje daya.

Ki rika sha kadan kadan kamar tsawon kwana 7 zaki bada labari.


Za a iya yima Amarya Mai shirin yin aure haka ma Uwargida ma zata iyayinsa.

Comments