Main menu

Pages

YADDA YA ZA A MAGANCE DUK WASU CUTIKAN CIKIN BAKI CIKIN SAUKI

 Yadda za a Magance Amosanin baki, Wana ya kunshi kurajen baki, ciwon bakin da Kuma wari.


Amosanin baki na nufin (mouth disorder) ma'ana rashin lafiyar da ta shafi tun daga kuraje, ciwon baki dakuma warin baki. Duk wanda Allah yajarabta da wannan lalura duk yadda ya wanke bakinsa ko yayi asawaki ko brush da maclean bakinshi ba zai daina wari ba domin akwai kwayoyin cutar bacteria acikin bakinsa idan suka hadu da abinci zasu rika wari wanda hakan yakan takurama mutane masu laluran har yakai ga basason magana cikin mutane.

Cikin ikon Allah yau zamu sanar da yan'uwa wannan magani indai aka jarabashi to Insha Allah za a ga biyan bukata na farko za a samu zuma, garin kaninfari garin magarya da kuma garin bagaruwa. 

Za a dafa ruwan zafi cikin kofi sai azuba karamin kowane cokali cikin ruwan zafin sai zuma cokali biyu sai amotsasu sosai. Za a rika kuskure baki ana zubarwa sau biyar akowace safiya bayan an kuskure sai asha rabin kofin ruwan 

Insha Allahu kowane irin amosanin bakine za a warke Allah yasa mudace Ameen.

Comments