Main menu

Pages

YADDA AKE AMFANI DA ZOBO WAJEN MAGANCE MATSALAR RASHIN HAIHUWA

 Yadda Ake amfani da Zobo Wajen magance Matsalar Rashin Haihuwa ga Mace ko Namiji

Zobo wani sanannen ganyene da mutane ke tafasawa ko jikawa asha kuma za a iya kwadashi aci wanda mafi akasari ana nomashi ne a arewachin Nigeria. 


Wannan ganye da ake sha yana kunshe da wasu muhimman sunadarai wadanda suke taimakwa sosai wajen bunkasa lafiyar dan adam.


Wadanda suka san amfanin zobo mafi akasari sunfi amfanin dashi wajen bunkasa yawan ruwan, (sperm count ) ga namiji  wanda rashin yawan ruwan sperm na daya daga cikin abubuwan da kesa rashin haihuwa ga maza.

Bayan haka zobo yana kashe kwayoyin cutar bacteria dake kama farjin mata da kuma infection din da ke kama mahaifa wanda shima barazanane ga mace mai neman haihuwa.

Yadda za ayi amfani da Zobon wajen samun haihuwa 

Duk mai neman haihuwa mace ko namiji ko son magance wasu cututtuka da ake iya dauka wajen saduwa to za a rika dafa zobo da citta bayan sun dahu atace adan kara ruwa asha kofi daya kafin aci komai kullum da safe.

Jan Hankali

(1) Baa sha da sukari 

(2) Mace mai yaron ciki ko tsohon ciki bata shan zobo domin yana kunshe da wasu sunadarai daka iyasa zubewar cikin kokuma a haifi jaririn kafin ya isa haihuwa.


Allah Ya datar damu dukkan Alkhairi Ameen 

Comments