Main menu

Pages

WASU HANYOYI BIYAR DA ZA KI BI WAJEN GYARAN FUSKA

 Hanyoyi biyar da za a bi don gyaran Fuska tayi kyau

⇒ Za a iya hadin ruwan lemun tsami da na zuma sannan a shafa a fuska ko jiki, domin inganta hasken fata da karfafa fatar jiki da kuma hana fesowar kuraje._ ⇒ Akwai hadin ayaba da kwaiduwar cikin kwai da  man zaitun. Idan aka yi wannan hadin, sai a shafa a fuska na tsawon minti ashirin sannan a wanke, shi ma wannan hadin domin gyaran fatar jiki da kuma na fuska ne.⇒ Hadin ruwan lemun zaki da ruwan kwai da kuma kurkum na da matukar muhimmanci sosai domin yana taimakawa wajen gyaran fata, musamman ma ga amare.⇒ Garin bawon lemu wanda sai an busar sannan a daka a tankade sannan a hada da ‘baking soda’ shi ma yana magance cututtukan fata sosai.⇒ Akwai hadin ruwan kwakwa da garin bawon lemun zaki da kuma madara. Wannan irin hadin na sanya fata sulbi sosai.

Comments