Main menu

Pages

MUHIMMAN HANYOYIN DA ZA A BI DON KARFAFA LAFIYA LOKACIN SANYI

 



Muhimman Hanyoyin da ya kamata a bi don Karfafa Lafiya lokacin Sanyi.

Dazaran ƙarshen shekara ya nufato, Sai a shiga yanayi na sanyi. Hakan na iya zama kalubale ga lafiyar mutum ta hanya mafi sauƙin kamuwa da mura, tari, bushewan labba, da sauransu.





A kula da waɗan nan shawarwari:

1. A yawaita shan ruwa sosai


2. A yawaita wanke idanu akai akai domin gujewa kamuwa da ciwon ido.


3. A yawaita amfani da abin rufe fuska da hanci (Facemask).


4. A takaita zirga-zirga a waje sai dai wanda ya zama dole, mai mahimmanci.


5. A yawaita sa kaya masu ɗan kauri, ko rigunan sanyi domin sanya dumi a jiki.


6. A yawaita rufe tagogi da kofofin domin takaita shigowar kura daki.


7. A yawaita shafa mai a jiki domin dandashe fata kar ta bushe.


8. A yawaita shafa mai a labba domin kare su daga farfashewa ko tsagewa.


ABIN LURA: Wannan yanayi na iya tayar ma da masu ciwon Sickler da Athma ciwon su sosai. A kula.

Comments