Main menu

Pages

GYARAN JIKI GA UWARGIDA AMARYA KAI HAR MA DA 'YAMMATA

 Gyaran jikin Uwargida, Amarya da 'Yanmata don samun Fata mai kyau santsi da goge gautsi.


A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sannan a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20 sannan a wanke da ruwan dumi.
 Lemun tsami da sukari na taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki sannan suna sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku sannan a wanke.
 A yi amfani da daya daga cikin ababen da na lissafo. Kada a shafa a lokaci guda don amfani da abubuwa da yawa na haifar da kuraje.


Allah Ya sa a dace idan kin karanta ki tura ma wata ta karu.

Comments