Main menu

Pages

ILLOLI GUDA TAKWAS DA SHAN RUWAN SANYI KE HAIFARWA

 



Illoli takwas da Shan ruwan sanyi ke haifarwa Lafiyar Dan Adam.


1. Tsaida Bugun Zuciya:- Bugun zuciya shike gyara dumin jiki da daidaita numfashi to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. Ko kunsan yawancin yan film na kasar indiya da yan ball da boxing da wrestling tsayawar bugun zuciya ke ajalinsu kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi yayin da suke aikine yake jawo musu.





2. Lalata Tsarin Kayan Ciki:- Shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji guri daya sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri hakan kan jawo matsalar hanji ulcer kenan ko kuma tashin zuciya. Yawancin masu shan ruwan sanyi suna yawan zubda yawu ko tashin zuciya ko saurin kullewar ciki.





3. Dauke Karfin Jiki:- Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji dadi amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon cewa yayinda ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai na'urorin jikin sunyi kokarinsu na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin hakan yanasa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi. Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman farkon zazzabi a hankali kuma sai kuji ya daina.





4. Ciwon Makogwaro da dakushewar Murya:-

Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro har sukai ga basa amfaninsu mai kyau ga mai sha yakai shekaru arbain sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya ko muryar ta fashe kwatankwacin mashayin taba.





5. Ciwon Hanta da Koda:- Dukansu suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu don haka yayinda bawa ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara kasa in haka ta samu mutum ya shiga matsala.





6. Busar da Ruwan Jiki:- akwai na'urori a jikin dan Adam da aikinsu shine sadar da ruwa ko ina a jikin mutum ta yanda ko ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi. To wadannan na'urori sukan yi sanyi sakamakon ruwan sanyi sai su zama so weak.




7. Matsalar Ma'aurata:- Wannan abune tabbatacce harga likitocin zamani cewa shan ruwan sanyi yana raunata mazantakar namiji yana kuma busar da mace in mahaifarta nada rauni yana iya hana haihuwa. Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin inzali ko kuma ya rage masa kuzari. Yana dauke ni'imar jiki su zamo basa gamsuwa da juna.





8. Basir da ciwon Kai na gefe Migraine :-

shan ruwan sanyi yanda nace muku yana tattare hanji hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida sai ya hadu da basir.

Sannan yana kawo ciwon barin kai wanda ake cewa migraine. Shi kuma migraine yana kashe jijiyoyin ido a daina gani sosai in yayi nisa har hauka yana sawa.

Allah Ya kyauta Ya sa a rage Shan ruwan sanyi

Comments