Main menu

Pages

HANYAR DA YA KAMATA KI HADIN CICCIBIN SANIYA KO NA AKUYA

 



Yanda Ake ingantaccen hadin Ciccibin Saniya ko na a kuya da amfaninsa a jikin Mace.


Ba sabon abu bane ganin ciccibi a wajen masu tallan maganin mata saidai yanda ake hadashi akwai dan wahala musamman idan baki taba gani ana yi ba domin zaki iyayinsa ya baci kuma zai iya bata miki ciki shiyasa ba aso mace me ciki tarinka cinsa.



Nayi kokarin tabbatarwa da sahihancin wata hanyar da zaki iya yinsa cikin sauki da kanki idan har kina bukatarsa




Ki saka asayo miki gaban saniya kona akuya kowanne anayi dashi amma danyensa saiki yanyankashi ki wanke ki dora akan wuta dama kin daka ridi wanda aka soyashi ki zuba zaki iya saka nonon akuya kona rakumi sannan kisaka garin kanun fari saiki saka duk wani kayan miya yanda zai miki dadi saiki barshi saiya dafu saidai anaso kiyi yanda romon zai zama dan kadan shi wannan naman da romon duk zaki cinye 





Idan kuma kinaso ki soya shi saboda ki ajiye shi wannan yafi wahala amma yafi aiki ana bukatar kisamu ridi da gyada ki soyasu sama sama saiki saka kanun fari sannan ki  dakasu su zama gari saiki jika da ruwa ki gauraya ki tace ruwan ake bukata lokacin soya naman domin idan kika yayankashi saiki zuba wannan ruwan saiki dora akan wuta kina jujjuyashi anaso kiyi yanda wannan ruwan yana karewa naman ya kusa soyuwa saiki saka man gyada ya karasa soyuwa shikenan kin gama kowanne lokaci kina iya cinsa.




Amfanin cin wannan nama ajikin mace yanada muhimmanci saboda yana saka gaban mace ya ciko ya kumbura ciki kuma ya matse sannan yana karawa mace ni ima da dandano ki jarrabashi kiji yanda akeji.

Comments