Main menu

Pages

DABI'U 14 DA MACE MAI AJI DA KAMUN KAI TA SUFFANTA DASU.

 Siffofin da za a gane Mace Mai Aji da kamun Kai.


__Itace macen da tasan darajar kanta da kuma addinita ta hanyar gujema duk abinda zai taba mutum cinta.


__Itace macen da bata shiga abinda babu ruwanta domin gudun kar arainata.


__ Itace a koda yaushe take suturta jikinta domin tana matukar kishin kanta.


__Itace wadda bata tara samari ko kuma kawaye barkatai saboda gujema kananan maganganu  ko kuma a wulakanta ta.


__Itace macen da bata daukan raini don ba ta raina kowa itama bataso a rainata.


__Itace waddda bakajin hayaniyar ta a inda ake yawaita surutu don tafi kowa kishin muryanta .


__itace wadda bata saka hotunanta a social media saboda tana matukar tsoron abinda zaisa aga surarta


___Itace mace mai girmama duk wadda ya girmamata don tasan darajar su koda akwae wa'inda basa sonta.


__Itace komin sanda takema namiji bata bari har yaga fuskar da zaiyi wasa da sasan jikinta.


__Mace mai aji kana iya samun soyayyarta  ammah ba cikin sauki bane zata iya bari ka  shawo kanta.


__Mace mai aji takan koma mara aji a lokacin da take matukar sonka hakan nafaruwane saboda tunaninta kaine zaka aureta.


__Itace mace mai qualityn da kowani namiji yake mafarkin ganin ya aureta.


__Banbancin ne tsakanin jan aji da kuma girman kai da mace keyi ammah saika sa hankali  gami da tsaida tunnaninka waje daya sanan ka nazarta.


___Yar uwa ki kasance mace mai aji koda kuwa mutane xasuyi ta sukarki da bakaken maganganu akanki hakan shawarace kyauta.

Comments