Main menu

Pages

BANKIN CBN YA KARA YAWAN KUDIN DA ZA A NA FITARWA AKAN 20K

 



Babban Bankin Nigeria (CBN) ya Kara yawan kudin da za ana fiddawa akan 20k 

Ƴan Najeriya sun yi ta mayar da martanin kan sauyin matakin babban bankin ƙasar, CBN na ƙara yawan kuɗaden da za a iya cira a banki.



Lamarin ya yi wa wasu daɗi amma da dama na ganin sauyin matakin a matsayin "La ba a sa", wato babu yabo babu fallasa.



A ranar Laraba ne CBN ya sanar da cewa ya ƙara yawan kuɗaɗen da ɗaiɗaikun mutane za su iya cirewa a banki daga Naira 100,000 a sati zuwa 500,000, yayin da kamfanoni za su iya cire Naira miliyan biyar maimakon N500,000 da aka sanar tun farko.



Sauyin na CBN na zuwa ne bayan matsin lamba da sukar da ya sha daga ƴan ƙasar da dama, ciki har da majalisar wakilai da kuma masana



Cikin waɗanda suka bayyana jin daɗinsu da sauyin har da masu sana'ar POS da kuma masu tsokaci a shafukan BBC Hausa na sada zumunta.



Wani mai sana'ar POS a jihar Kano da BBC ta ji ta bakinsa ya ce sauyin da kaa samu na ƙara yawan kuɗin da za a dinga cira a bankin "ya ɗan" faranta musu rai.



"Amma ba dai sosai ba kamar yadda ake yi da. Mu da a matsayinmu na ejen muna cire kudi a banki ba ƙayyadewa, ko nawa ne muna cira.



"Sai dai duk da haka ƙarin da aka yi ɗin zuwa naira 500,000 daga N100,000 shi ma ba laifi, amma da so samu ne a ƙara ko da zuwa miliyan ɗaya ne a sati.



Mutumin ya ce a duk rana yana hada-hadar kudi har naira miliyan ɗaya ko sama da haka.



Shi ma wani mai POS din ya ce ya ji dadi da aka samu ƙarin, "saboda naira dubu ɗarin da aka ce za mu dinga karɓa a sati da farko to zai sa kasuwancinmu ya samu tangarɗa.



"Wannan ƙarin ya yi mana, amma da so samu ne ko miliyan ɗaya a mayar da shi, amma haka

Comments