Main menu

Pages

ABUBUWA GUDA 6 DA DUK BUDURWA KE BUKATARSU WAJEN WANDA ZATA AURA

 Wasu Abubuwa Guda 6 Da Duk Budurwa Take Bukatarsu Wajen Mai Sonta.

Akwai maza da zaran sun fara soyayya da mace sai nan da nan a kasa su saboda rashin sanin wasu dabarun da zasu iya mamaye zuciyar wacce suke so. Irin Waɗannan mazan har zargin kawunan su na ganin kodai suna da wata matsala ce ta ɓõye. Sam abun ba haka yake ba. Kawai rashin sanin dabarun mamaye zuciyar macen da kake so ne yake sa har wani namijin ya maka kwace.

Ga wasu dabaru guda shida da duk mace ke bukatarsu wajen masoyin ta domin samun Mallakar soyayyar ta.


1: Sauƙi kai: Mace tana son namiji ya zama mai sauƙi kai ba mai fada ko mai takura mata ba. Muddin zaka nunawa budurwar ka sauƙi kai cikin lokaci kana iya sace zuciyar ta.2: Alfahari da ita : Macen da kuke soyayya tana so taga kana alfahari da ita a duk inda kake. Tana son taga kana saka hotunanta a DP dinka ko status dinka ko yawan ambata sunanta. Duk mace da take samun waɗannan wajen saurayin ta cikin sauƙi zai mamaye zuciyarta.
3: Lokaci. Muddin kana baiwa macen da kake soyayya da ita ishenshen lokacin zama ko hira da ita, tofa da matukar wahala wani ya iya hamɓareka cikin sauƙi. Mata suna son a basu lokaci, suna son ganin suna tare da abar kaunar su a lokaci zuwa lokaci.
4. Himmar Aurenta: Duk macen dake sonka na gaskiya bata da wani buri illa taga cewa ta aure ka. Muddin taga cewa kana kokarin kun yi aure ta hanyar himmatuwarka wajen shirye shirye da tsare tsare domin hakan ya yiwu, to fa kana kara samun wajen zama ne a zuciyar ta.
5: Nuna Mata Kula. Muddin kana son kaga ka mallaki soyayyar mace ya zama wajibi ka zama mai nuna mata matukar kulawa. Mata na son suga mai son su yana yawan kiransu a waya, tura musu sakonnin tex, da kuma kula da bukatunsu wanda zasu iya fitowa fili su fada da waɗanda zaka fahimci suna bukatarsu.
6. Kyauta. Hanya mafi sauki da zaka iya sace zuciyar mace da shi kyauta shke kan gaba. Haka kuma hanya mafi sauki da za rabaka da macen da kake so shine ayi amfani da rowarka.


Don haka namiji mai hali ko ɗabi'a na rõwa, yana da matukar wahala ya iya samun soyayyar mace 100/100.


Da fatan maza masoya sun fahimci darasin kuma zasu yi amfani dasu.

Comments