Main menu

Pages

YANDA ZA A MAGANCE FITSARIN KWANCE GA MANYA DA YARA

 Hanyar da za abi don magance Matsalar fitsarin kwance ga Manya da Yara

Cutar fitsarin kwance lalura ce wacce take damu wasu yan uwa, yayin da aka sani cewa yara ne suke yin wannan Sanadiyyar rashin wayo da hankali, amma a gefe guda zaka samu babba wanda yake da shekaru ya balaga amma bai dena fitsarin kwance ba.
Akwai matsaloli da yawa da suke haifar da wannan damuwa Musamman ga manya wadan da shekarun su suka kai lokacin denawa amma basu dena ba.
Kadan daga wasu abubuwa da suke kawo matsalar fitsarin kwance ga Manya.

1. Matslar Cancer

2. Cutar mafitsara(uti)

3. Toshewar wani sashe na hanyoyin mafitsara (A blockage or obstruction in your urinary tract)

4. Matslar Hormones

5. Wanda yake da karamar mafitsara.

6. Masu fama da ciwon suga wandan da basa under control, da dai sauran su.
Hanyar da za a bi don magance wannan matsala

Da farko dai za a nemi wadannan abubuwan

1. Saiwar Gwanda

2. Gawayi

3. Sukari.
Za a samu wadan nan abubuwa saiwar zaa wanke ta a debi daidai gwargwado, za a samu gawayi mara yawa da sukari shima daidai misali.Za a hada da ruwa a jika da safe zuwa dare za a rika tsiyayar rabin kofi ana sha bayan an tace.
Ana sha ana kara ruwa tsawon sati 2 insha Allah za a samu waraka da yardar Allah.


Allah yasa mu dace.

Comments