Main menu

Pages

YANDA SUNADARIN SUKUDAYE KE RASHEN KASHE MASHAYAN TA

 MADARAR SUKUDAYE: Sinadarin da ke tashen kashe mashayan ta Arewa, bayan ya nukurkusar masu da huhu, hanta da zuciya


Ba a yanzu ne sinadarin MADARAR SUKUDAYE ya fara kashe matasan da ke shaƙar sa a matsayin sinadarin da ke bugarwa ba. Sukudaye da mashayan sa sun daɗe su na bugar da juna. Yayin da matashi ya shaƙa ya bugu, ya yi mankas, shi kuma sukudaye sannu a hankali sai ya fara nukurkusar matashi.

Farko dai bugar da shi zai fara yi, ta yadda idan yaro ya na magaro, wani ko buta cike da ruwa ba zai iya ɗauka ba.


Wanda sukudaye ya bugar, magana ma gagarar sa ta ke yi, ballantana ya tashi ya yi tafiya. Da wandon sa zai saɓule, za ta yiwu ko ɗaura tazugen ba zai iya ba.

Cikin 2005, fitaccen ɗan wasan finafinan Hausa da ake kira Katakore ya yi mutuwar ba-zata.


Ya fita gida da dare tare da abokin sa zuwa wurin hirar da su ka saba fita daga gidan su da ke Unguwa Uku, Gabas da Tashar Motar Unguwa Uku, a Kano.

Cikin talatainin dare abokin Katakore ya maida shi gida a wani halin da bai san inda ya ke ba. Ya riƙa kyara amai, wanda zuwa wayewar gari Katakore rai ya yi halin sa.


‘Yan uwan Katslakore sun shaida wa wakilin Mujallar MUDUBI a lokacin cewa, Katakore lafiya ƙalau ya fita gida bayan sun ci abincin dare. Sai dai kuma abokin fita yawon na sa ya shaida masa cewa ya sha sukudaye a inda su ka fita hira.

Shekaru fiye da 15 kenan, yayin da kama daga likitoci da jami’an hana shan ƙwaya da kowa ya san illar madarar sukudaye, wannan bai hana ƙara yawaitar safarar sinadarin da shaƙar sa a garuruwan faɗin Arewa ba, musamman a Kano, inda ake kasuwancin sa da shan sa fiye da sauran garuruwa.


Kwanan nan madarar sukudaye, wanda a Turance ake kira Metheylene Chloride, ya kashe mijin wata mata mai suna Fatima, wanda ya mutu ya bar ta da ‘ya’ya biyu a Kano.
Mijin na ta mai suna Mohammed ya na sayarwa kuma ya na sha kafin sinadarin ruwan ya zamo ajalin sa. Hatta ƙanin mijin ta shi ma ya na shaƙar madarar sukudaye.


“Da farko miji na ya tsani sukudaye, kuma ya tsani mai sukar madarar sukudaye. Amma ban san yadda aka yi ba, bayan mutuwar ƙanin sa, sai shi ma ya riƙa tu’ammali da madarar sukudaye, har shi ma ta zama ajalin sa.” Inji Fatima.


Fatima cewa ta yi wata rana mijin ta ya shi ga ban-ɗaki ya daɗe bai fito ba. Da ta shiga sai ta sake shi a nuske, ya yi mankas. Daga nan ya galabaita, bai san inda ya ke ba. Bayan ‘yan kwanaki ciwo ya yi tsanani, kuma ya ƙi zuwa asibiti. A haka ya mutu a gida.” Cewar Fatima, kuma likita ya shaida masu cewa madarar sukudaye ce da ya riƙa shaƙa ta kashe shi.”

Aiki Da Aika-aikar Madarar Sukudaye A Jiki:

Binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar da cewa duk da dai babu ƙididdgar yawan da waɗanda madarar sukudaye ke kashewa a Arewacin Najeriya, sinadarin ya kashe da dama a Kano, Adanawa, Gombe, Borno da Bauchi.
Madarar Sukudaye na bugar da mashayi. Zuƙar ruwan ake yi a jiƙa tsumma ko hankici a riƙa shaƙa, ana wuwwurga idanu. Daga nan jiki zai yi liƙis, yaro ya yi mankas bayan ya nuske, ta yi yadda ko taɓarya aka ce ya ɗauka ba zai iya ba. Tsayuwa ma kan yi masu wahala sosai, tilas sai an zauna wuri ɗaya ba uhm ba umhmhm, har tsawon sa’o’i da dama. Sai bayan jiri ya daina ɗibar yaro sannan zai tashi ya na tafiya da kyar, kamar birin da yunwa ta rarake.

Illar da madarar sukudaye ke yi wa jiki sun haɗa da lalata huhu, lalata hanta da kuma lalata zuciya ta na kuma yi wa idanu illa.


Wata likita a Asibitin Malam Aminu Kano ta shaida wa wakilin mu cewa madarar sukudaye “na haifar da sankarar huhu,” inji Likita Hassana Abubakar.

Wakilin mu ya ci karo da wani yaro ɗan magaro a cikin Sabon Gari Kano, wanda ya nuske da madarar sukudaye.


“Iyaye na Kano su ke, amma ba a gidan mu nake zaune ba. Ni duk lokacin da na shaƙi madarar sukudaye, sai na manta da duk wata damuwa.”


Irin haka yawancin unguwanni su ke Kano, inda za ka riƙa ganin matasa ‘yan jagaliya rukuni-rukuni su na shaƙar madarar sukudaye.

PREMIUM TIMES ta gano inda wani babban dillalin madarar sukudaye ya ke a Jakara ‘Yankaba, inda ake sayar da sinadarin ruwan birjik. A kasuwar akwai yara matasa danƙam yawancin su bugaggu, inda ake sayar da kayan rafta.


PREMIUM TIMES ta gano kasuwar da ake sayar da madarar sukudaye a Legas da kuma inda ake haɗa shi. Daga can ake loda shi zuwa Kano.

Wakilin mu ya yi shigar burtu, ya tambayi farashin madarar sukudaye lita 25 Naira 48,000. Duro ɗaya kuma Naira 350,000.


Ya je a matsayin ɗan sari ne daga Kano, ya saya a kan titin Ojo Giwa Street, Unguwar Tinubu a Legas, ya lodo cikin doguwar motar matafiya zuwa Kano.


Ya biyo motar ya ga yadda direba ke bai wa jami’an tsaro cin hanci ya na wucewa da duk irin abin da ya ɗauko, ba tare da an bincike shi ba.

Comments