Main menu

Pages

GUDUMMUWAR DA MATA KE BAYARWA WAJEN MUTUWAR AURE A YAU

 Da Sa Hannun Kowa Wajen Mutuwar Aure A Yau; Bangaren Mata wajen gudummuwar da suke bayarwa wajen mutuwar aure


  

A kullum ana fara ambaton a zabi mace ta gari a farko saboda muhimmancin mace a cikin al’umma.Kowanne namiji yana fatan ya sama wa ‘ya’yansa uwa ta gari ko da kuwa shi ya san halinsa yana da nakasu.Ya yin kuwa zaben mace ana son a samo ta gari duk lokacin kuwa da aka sami akasin haka shi ke haifar da matsala ko bayan an yi auren.Wasu za su iya cewa to me yasa matsalar ba ta hana auren ba?
Haka ne amma me yasa matsalar ba ta hana auren mutuwa ? Dalilin da yasa hakan shi ne kaddara da kuma rufewar ido a soyayya ko kuma girman wani ko wata makusanci ko wanda ya yi dalilin auren.Amma daga lokacin da zama ya yi zama sai a fara tunanin neman mafita.

Ta yaya maza za su gane mace ta gari?

Mace ta gari ita ce ta siffantu da kakkyawar dabi’a da halaye da kamala kallo daya za a iya gane tarbiyyarta da kokarin da iyayenta suka yi wajen ba ta tarbiyya. Mace ta kwarai ita ce wadda kowanne namiji mai hankali zai yi fatan a ce tana gidansa ta zame masa sanyin idaniya ta zama al-mar’atissaliha da Annabi Muhammad (SAW) yace ta fi duniya da duk abin da yake cikinta.

 Mace ingantacciya ita ce dai matar da kowanne namiji zai so ya sami zuriya da ita.

Aure da dama a yau yana mutuwa amma sai a rasa dalilin mutuwarsa a yi ta dorawa wani bangare na daban wanda wannan kuskure ne babba. Abinda ya kamata a lura da shi shi ne in an bi ta barawo sai a bi ta ma bi sawu . 

Maza suna da nasu nakasun da rashin hakuri amma kuma matan ma akwai gyara a yadda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum a wani lokacin yana sabawa tarbiyyarmu ta Hausa/Fulani yana sabawa al’adunmu da addininmu.


 Bahaushe tun tasowarsa yana da tarbiyya da tsari managarci don yi wa ‘ya’yansa tsani na samar da al’umma nagarta. Daga cikin abubuwan da mace ya kamata ta zama don kama hanyar mace ta gari akwai:-

- Kamilalliya:

Mace kamilalliya ita ce wadda take me kamun kai ba ta shiga hayaniya, za ka same ta ko da cikin ‘yan’uwanta mata ba ta da rawar kai bare a gun maza .Kamilalliyar mace za ka same ta ba ta da shigewa maza ko da muharramanta ne kullum in ka ganta da namiji da ya zama dole sai an gansu saboda alakar karatu ko aiki ko wata hujja ta daban. Za ka ganta a tsorace tana kaffa-kaffa.In kuma ta sami wanda take so yana cikin matakin farko da mace ya kamata ta fara nunawa a gun duk wanda take so su kulla mu’amala take fatan dorewarta zuwa aure.Hanyoyi da dama ya kamata mace ta bi don tabbatar da cewa ita mai kamun kai ce.


 

Mata a yau a tunaninsu na yaudarasu don yadda suke ganin maza na haba-haba da mata ba tare da nuna wani zabe ba to su sani iyakar ta waje ne amma matar ta aure mai kamun kai ake nema. 

Sutura:

Sutura ita ce abin da ka sanya a jiki don kare tsiraici. Abu na farko da kan ja hankalin namiji ga mace har ya gane ajin da zai ajiye ta shi ne irin suturar da ta saka jikinta


Mata a yau suna tunanin bayyana tsiraicinsu shi ne hanyar da za su iya janyo hankalin namiji gare su har ya gane kyan wani bangare na jikinsu da zai kai su ga aure. Ko kuma wata wayewa ce da ci gaba saka matsattun kaya.Wannan babban kuskure ne namjin da wannan zai dauki hankalinsa har ya yi tunanin ku yi sabo to tabbas sai dai soyayya wanda a karshe da-na-sani ne zai biyo bayan haduwar. Macen da ke sanye da suturar mutunci ake nema a aura ba ballagaza da ta gama nuna kanta a titi ba.


Surutu:

Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai macen kwarai ba a santa da daga harshe ba ko da a cikin ‘yan’uwanta mata ne bare kuma maza.Wata matar tana tunanin in ta shiga dandazon maza ta daga muryarta da zakewa shi ne zai janyo hankalin namiji kan ta.

 

Mace mai kamewa da karancin Magana tana da tasiri kwarai a lokacin da ake batun aure da ma bayan an yi auren.Sau tari matsalar da ake samu na shigar aikin assha tsakanin abokin miji ko kuma wani dan’uwan mijin tana fara kulluwa ne ta yadda mace take sakin jiki ta yi ta surutu daga nan sai a gane ba ta da tsada da an yi mata karamar Magana za ta fada.

- Kunya:

Kunya na da matukar tasiri a rayuwar yau da kullum . Mace da kunya da kara da kawaici aka santa. Bahaushe ba ya son mace marar kunya don haka yake tarbiyyantar da ‘ya’yansa kunya tun suna kanana. Mace marar kunya ba ta farin jini wajen al’ummar da suke da mutunci hatta a gidan aure in har yarinya ta zama marar kunya ba a taba samun jituwa da iyayen miji ko danginsa. A kwai alamomi da suke nuna lallai wannan tana da kunya ciki akwai:-

- Ciye-ciye /Tauna

Mata a yau sun zubar da kyakkawar al’adar nan ta kame kai wajen ciye-ciye a kan hanya ko gaban samari. Mace mai ciyeciye da rashin kimtsi ko ga sa’anninta mata ba ta farin jinni bare maza. Ko kuma ta yi ta taunar cingam duk wannan alamun rashin kunya ne.

-Roko

Roko shi ma wata hanya ce ta nuna rashin kunya da mata kan dauka hanya wayewa. Duk matar da ta fiye roko da ba- ni ba- ni tana kashe wa kanta wata daraja ne ga mai sonta kuma in har mace ta fiye roko to fa tana nunawa wannan da zai aure ta irin zaman da za su yi. Hali na farko da za su sa a ran su in har suka kai ki gidansu ba za ki iya hakuri da samu da rashi ba sannan duk randa babu ba za ki iya rufa wa zamantakewar asiri ba. Roko ga mace babbar hanya ce ta zubar da mutunci.

- Kallo

A kallo kadai a na iya gane mace mai kunya da rashinta.Yadda mace za ta kafe namiji da ido yana nuna kunyarta da rashinta musamman idan yana wata magana. Mace an fi sanin ta da risnawa.


 
- Rashin Jan Aji

Mace ta kirki da jan aji da kamewa aka santa.Kar ki zama mai girman kai amma ki zama kin san darajar kanki. In har za ki zama arha kowanne namiji ya kira ki ba tantancewa ki je kowa yake bukatar jin hira da yawo ke za a zo nema a tafi da an ce ana sonki to fa ke kasuwa ta bude ba sauran edcuse to fa kin kade ba ki sa dan-ba ba a wajen neman mijin aure ba ko da kuwa rabon ya rantse an yi auren to da wuya auren ya kai labari don ko bayan kina gidan mijin zai ke zargi da tunanin halinki na rashin jan aji da amsa kiran kowa.

- Makauniyar Soyayya

A duk lokacin da zafin soyayya ya ja ki ko dai ke don son da ki ke yi wa mijin ko don shi son da yake ikrarin yana yi miki ko ma don a tunaninki mallaka masa kan ki da ki ka yi shi ne matakin farko na wajibcin sai ya aureki to kin yi kuskure. Maza kalilan ke iya wannan halascin ga mata.Wasu matan ana yaudarar su ta hanyar kai kudin aure gidansu da an kai sai iyaye su aminta da wanda ya kai kudin su sallama masa yarinya ita kuma sai ta saki jiki wanda aure da dama da abin nema ya samu sai aure ya fara rawa kenan kuma ko da an yi auren wannan abinda ki ka yi sai a karshe in aka yi rashin sa’a ya janyo matsala duk kuwa da shi ne ma ya janyo hakan ta faru shi ya yaudare ki ya yi miki romon baka.

- Rashin Hakuri

Zama yau da gobe sai da hakuri Bahaushe ma ya ce tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa haka nan zo mu zauna zo mu saba don haka dole zaman tare dole a yi hakuri a kai zuciya nesa. Wajibi ne a ke yi wa juna uziri. Don haka a ke yin hakuri da juna a ke samar wa juna mafita.


In kuwa haka ne to da sa hannun mata a yau wajen mutuwar aurensu don duk auren da ba a yi masa ginshiki na kwarai ban a matar da za a aura akwai yi wu war mutuwarsa.


Allah ya nuna ma na next post inda za mu kalli bangaren maza su ma mu ga ta ina su kuma su ka sa hannu wajen mutuwar aure a yau.


SHARE TO OTHERS PLEASE KAMAR ANYI SADAKATUL JARIYANE

Comments