Main menu

Pages

YADDA ZAKIYI AMFANI DA BAWON AYABA WAJEN GYARAN FUSKA DA JIKI

 Sirrikan dake cikin Bawon ayaba da amfanin da yake ta fuskar gyaran jiki.

Karanta Sirrukan Amfanin Ɓawon Ayaba da Zasu Girgiza Ku

Bawon ayaba na kunshe da sinadarai masu dumbin yawa wadda ke da mutukar amfani ga lafiyar jiki. Bawon ayabar na kunshe da sunadarai kamar haka:

Patassium, zinc, amino, da vitamin Wanda zasu jiki ya samu lafiya cikin jiki. Kana bawon ayabar na taimako wajen gyran jiki da tsatso da kyau domin yana dauke sinadarin:

Carbohydrate, vitamin, B6, B16, antioxidant, mineral hade da magnesium wadanda ke raya kwayoyin halitar jiki, maganin cizon sauro, kurajen jiki gami da sanya hasken hakori.

Binciken masana kimiyyar sinadaran ‘ya’yan itatuwa da aka gabatar a shekara ta 2011 da 2018 yayi nuni zuwa ga tarin sunadarai da magunguna da bawon na ayaba ke yi.

Duba da irin muhiman sunadarai musaman antimicrobial, antioxidant da phenolic, bioactive kamar polyphenol, carotenoids sanan hadi da anti-inflammatory wanda ke sa kunar rai.

Amfanin bawon ayabar wajen warkar da yankwanar fuska

Yadda za a yi domin maganin yankwanar fuska a hada bawon ayaba da gwaiduwar kwai a cakuda su sosai.

- A shafa hadin a fuskar sarai

- A bar shi na tsawon dakika 5 (minti)

Sanan sai a wanke fuskar za a maimaita hakan sau uku a sati


    Domin goge tabo (miki) 

Yadda za ayi domin goge tabo, a daka bawon ayabar a shafa a kan tabon a bar shi na tsawon sa’a guda ko dukkan dare.

A maimaita hakan kullum


Domin magance kaikayin fata

A shafa bawon ayaba a daidai yadda yake kaikayin a bar shi na tsawon dakika 10-15

Sanan a wanke

Yadda za ayi domin magance kurajen fuska (pimples)

Shafe illahirin fuskar a bar shi har tsawon dakika 5-10 Sanan a wanke fuska

Ana shafawa sau biyu a rana.

Magance dabbbare dabbaren fata

Domin magance dabbare-dabbaren fata, a kankaro wanan farin na jikin bawon ayabar sai a hada shi da Aloevera (aleo vera) sanan a na shafawa. sanan ake shafawa domin samun hasken fataAbubuwan hadawa

Bawon ayaba guda daya

Cukali 2 na garin alkama

Cukali 2 na sukari

Cukali 1 na danyar madara

Sai a hada

Bayan an kirba bawon ayabar a hada da garin sukarin da na alkama

Sanan a shafa a jiki duka sosai a wanke bayan minti 20-30

Domin sa laushin fata

Yadda ake hadawa

A nuke bawon ayaba sanan a shafe fuska amma a kiyaye kar ya shiga baki ko idanuwa, sannan sai a wanke fuska da ruwan sanyi.


Domin magance maikon fata

Yadda ake hadawa

Nike bawon nunanar ayaba sai ki hada da shi da zuma cukali daya da rabin cikin cokali na lemon

Sai a shafe fuska.


Domin goge hakora suyi haske tas

A gutsiri bawon ayaba, a shafa shi a hakori

A bar shi na tsawon minti 10-15

Sanan a goge shi

A tabbatar da yin amfani da bawo mai kyau kuma kar a ajeyi shi a firji.Comments