Main menu

Pages

AMFANIN GANYEN SHUWAKA GUDA GOMA GA LAFIYAR DAN ADAM

 



Amfanin Ganyen Shuwaka guda shida ga Lafiyar Dan Adam

Mutane da dama kan yi amfani da shuwaka ne kawai a matsayin ganyen miya, amma in an yi amfani da ganyen yadda ya kamata, akwai magunguna da dama a jikinsa. Masana harkokin bincike kan magunguna  sunyi matukar bincike kuma sun gano cewar ganyen shuwaka na dauke da sinadarai da dama da ke magungunan cututtuka daban-daban kamar haka;


 



1. Ciwon Hanta; Ganyen shuwaka magani ne mai kyau na ciwon hanta ana amfani da shi kamar haka: A samo abarba da ba ta nuna ba, sannan a samo ganyen yazawa (cashewy guda goma, sai cikin tafin hannu na ‘ya’yan auduga, sai kwalba goma na ruwa wanda za a tafasa. A rinka sha cikin babban cokali daya kullum har kwana goma.





 2. A Markada namijin goro guda 20 har ya zama gari sannan a zuba cikin ruwan lemon tsami (Lime juice) a kawo kwalba daya na zuma mai kyau a hada su duka a waje daya a gauraya. A rinka shan babban cokali daya (dessertspoon) sau hudu a rana har na tsawon watanni biyu.


           




 3. A Markade ganyen shuwaka guda 40 a zuba cikin ruwa mai kyau da ya kai lita 4 a rinka shan kofi guda sau 3 a rana har na tsawon watanni biyu. Wannan yana magani sosai na ciwon hanta, in ruwan ya dade ana iya sake wani sabon jikon.






4. Zazzabi A tafasa busasshen ganyen shuwaka (gram 10) a samo gram 25 na busasshen garin tumeric a dafa a cikin ruwa kofi daya har sai ya tafasa. Tun da duminsa sai a sanya zuma cokali daya, daga nan bayan ya huce sai a sha sau uku a rana. Yana warkar da zazzabi sosai.


           




 5. Sankara (Cancer) Kari (Kulun Da Ke Fita A Jiki) Shan ruwan da aka tatse daga ganyen shuwaka yana taimakawa wajen rage girman kari da jinkirtar da girman kwayoyin cutar sankara. Shan ruwan domin yana kara karfin garkuwan jiki.


 




6. Hawan Jini; Ruwan ganyen shuwaka na taimakawa wajen rage yawan gishiri a jikin mutum domin yana dauke da sinadarin ‘potosium’ mai yawa, a ciki.


Allah Ya Kara mana Lafiya

Comments