Main menu

Pages

YADDA ZA A MAGANCE CIWON HAKORI KOWANE IRI INSHA ALLAH

 
Yadda za a Magance ciwon Hakori kowane iri, Mai ciwo, girgidi ko kogo Insha Allah

 Yau mun kawo maku maganin ciwon Hakori, kasancewar mutane wasu na fama da wannan Laura.

 Kuma wannan fa'ida tana da karfi da tasiri sosai da sosai, abin bukata kawai a samu ingredients din ya zama Original.


 Abubuwan da za a nema

1. Man kaninfari (clove oil) 

2. Garin kaninfari (clove powder) 

Yadda za a hada;

 Idan hakurin ciwo yake ko rawa ko radadi,to sai a samu man kaninfari a dangwalo da auduga a lika a wajen zuwa minti sha biyar sai a  cire, ai  haka sau biyu a rana.

 Idan kuma yayi rami to sai a samu garin kaninfari kadan a kwaba shi da man kaninfarin, sai a dauki kadan a lika a wajen lokacin kwanciya bacci zuwa safiya a kuskure baki a zubar. 


Insha Allah duk mai fama da ciwon hakuri yayi amfani da wannan fa'ida da yardar Allah zai samu waraka. 

 Allah Ya sa a dace

Comments