Main menu

Pages

HADIN RIDI HAR KALA UKU DON KARIN NI'IMA

Yadda Ake sarrafa Ridi da sauran kayan Hadi don samun Ni'ima

1- GARIN RIDI: Zaa Samu kankana akasa kashi uku za’a dauki kashi daya daga cikin 3, sai a hadasu a zuba a cikin blander a markade, sai a zuba garin ridi a ciki, a zuba madara da zuma ki zuba wa angonki cikin kofi kisha ya sha. Wannan hadin yana kara ni’ima da maniyi, yana hana karnin dake fitowa,_

2 - HADIN RIDI Anso miji da mata su ringa amfani da wannan hadin domin Karin ni’ima yana kuma sa koda yaushe ta dinka bukatar mijinta kusa da ita_

1.Ruwan Kwakwa 

2. madaran peak 

3. Zuma 

4. Ridi 

Zaki hade su wuri guda ki ringa sha yana kara ni’ima sosai da sosai._

3 - Hadin Ridi (Karin ni’ima da kuzari) anso miji da mata su ringa sha domin motsa sha’awa._

1. Kanunfari 

2. Zuma 

3. Garin Ridi 

4. Nonon shanu Mara tsami


Ki dafa kanunfari da ruwan zafi idan ya dauko nuna (dahuwa) sai ki sauke ki sami garin ridi da nonon shanu mara tsami, ki hade guri daya ki gauraye. Ki saka a firiji ko ki saka kankara idan yayi sanyi sai ki sha. Wannan hadin idan kinyi sai kuma bayan mako daya za,a kuma yi_


Comments