Main menu

Pages

KALOLIN KAZAR AMARE HUDU DA YADDA AKE DAFA KOWACE

 
Hanyoyi hudu da za abi don dafa Kazar Amare

 Kaza ce da ke tabbatar da ni'ima a jikin mace sannan gaban mace ya ciko kuma tana saka mace ta Rika gamsarwa sosai ta yadda mijinta kowanne lokaci zai so ya sadu da ita haka kuma tana saka mace ta zama me sha'awa.

Yadda ake hada wannan Kaza kala-kala ne!

Ga wasu hadin da muka kalato

1- Kaza ta farko.

•Kayan hadi;-

•Kaza budurwa

•Nonon raqumi 

•Kanumfari 

•Minanas

•Yayan zogale 

•Geron mata 

•Dan bashanana 

•Ridi

•Man ayu

   Kazar budurwa ake samu Wanda bata taba kwai ba idan aka yanka a na so a cire hanjin da kai da kafa sannan a dafa ta da ruwa, idan  ta dahu sai a zubar da ruwan sai a zuba nonon rakumin, dama kin daka kanunfari da minanas da 'ya'yan zogale da geron mata da dan bashana da ridi sai a zuba a ciki ana so a saka man ayu kadan don ya zama shine man dahuwar, ko kuma a  gauraya shi da man sai kuma a zuba kayan hadi yadda zai  dadin ci.

 komai ana iya zubawa don yayi kamshi, to fa Kaza ta kammala.

     Wannan Kaza tana taimakawa wajen

Cikowar gaban mace ciki Kuma ya matse sannan ya tara ni'ima ga Kuma  dadin saduwa da gamsar da miji.


 Hadin Kaza ta biyu:-

kayan hadi;

•Kaza budurwa 

•Sassaken gamji

•Sauyar malmo

•Dan kumasau

•Minannas

•Gishirin gallo

•Sauyar baure

•Garin ridi

•Man ayu

Idan kaa dafa su aka tace ruwan sai a dauko budurwar kazar wanda daman an gyara ta sai a saka a cikin wannan ruwan a saka kayan miya da kayan kamshi sannan a saka man ayu kadan da garin ridi sai a  rufe a bar shi ya dahu, shikenan ta zama abincin ci, amma na mace daya ne, abun nufi ke kadai zaki cinye har da romon.


Hadin Kaza ta uku:-

Kayan Hadi;

•Kaza budurwa

•Ridi

•Harzar kabewa

•Minannas

   A samu ridi danye a daka shi ya zama gari sai a samu harzar kabewa ki zuba mata ruwan zafi a barta ta jiku sai a tace ruwan sai a zuba wannan garin ridin sannan a  daka minannas a  zuba garinsa a ciki to wannan ruwan shine za a dafa kazar a ciki amma a samu budurwar kaza bayan an  gyarata an cire kayan cikin sai a zuba idan da hali a samu farin gadali a daka a zuba a ciki z a iya zuba kayan miya yadda akeso a dafa ta ta dahu sosai sannan a sauke. Amma mace daya CE za ta cinye duka har miyar.


Hadin Kaza ta Hudu:-

Kayan hadi;

•Kaza wanda Bata Fara Kwaiba 

•Nonon Rakumi 

•Ridi 

Za a Yanka Kaza zare Hanjin Ba tare Da Kin  an yan ka ta gunduwa-gunduwa ba, Sai a zare Hanjin Ta Cikin Zunbutun Kazar Za a Wanke Ridin a shanya shi ya bushe Sai a daka shi Bayan an daka Sai a Zuba Garin Ridin Da Nonon Rakumi Acikin Zunbutun Kazar Sai a dinke Da Zare Da Allura Sai a Dafa Kazar Da Kayan Miya Kadan Da Nonon Rakumi A ciki Sai Ya Dahu Sai a ba mace ta ci ita kadai.

Dukkansu Hadi ne masu kyau za a samu yadda akeso Insha Allah.


Wannan shine yadda ake hadin dahuwar kazar amare, kowacce mace za ta iya kuma za ta yi saura kwana hudu a tare.

 Allah yasa a Dace.

Comments