Main menu

Pages

ABINDA KE KAWO (TEAR) QARUWA WAJEN HAIHUWA DA YADDA ZA A MAGANCESHI

 



Yanda Mace zata gane ta qaru wajen haihuwa, yadda zata gane ta qaru da yadda za a maganceshi

TEAR Wato matsalar kari da mata ke haduwa da ita bayan haihuwa yanayi ne dake zuwa bayan mace ta haihu. Tsaffin mata wadanda suka haihu da yawa zasu iya fahimtar sun samu kari a gabansu, amma mafi yawa yaran mata basu cika fahimtar hakan ba sai sun fara jin ko ganin wasu alamomi. 




Daga karshe unguwan zoma da mata masu ansar haihuwa sunfi kowa fahimtar mace ta samu kari. SHIN WANNAN MATSALA MENENE MAGANINTA? Kafin sanin maganin matsalar ya kamata asan wadanne alamomi za'aji ko gani a fahimci akwai alamar kari ga mace?




1, Tafiya bude.


2. Fitar iska


3. Budewar gaba


5. Zazzalowar mahaifa arika ji ko tabota ma.




Wadannan sune alamomin da mace zata ji kafin dubawa, ba'a daukan mataki ko yanke hukunci sai anje dakin haihuwa a buda a gani. 




Maganin wannan matsalar shine a dinke mace babu dubara ko kanikanci. wanda a da tsoro ke sa ake barin mata da matsalar abunda za a iya daukan shekara 10 da matsalar matukar ba dinkin akai ba.




Kauce ma faruwan hakan Kuma shine, duk lokacin da cikin yakai wata bakwai, to ana so Mai ciki ta dinga shafa Zaitun a qasanta kullum, hakan zaisa wajen yayi taushi sosai yadda idan aka zo haihuwa za a samu saukin tear din wato qaruwan.

Comments