Main menu

Pages

JARUMI DAUSHE, ZAI YU WUFF DA JARUMA ZARAH DIAMOND

 Jarumi Daushe zai yi wuff da Jaruma Zarat Diamond.


A yau mun leka cikin Kannywood inda muka ci karo da wadannan hotuna na pre - wedding na Daushe da Zarah Diamond, inda Ake cewa Jarumin fa zai yi wuff da Jarumar ne.
To Amma da aka fadada bincike sai aka fara tunanin wannan wuff din fa a Gidan Badamasi za ayi shi, domin kuwa kowa yasan cewa Daushe Yana cikin film din sannan yana yin waya da wata a boye baya so Matarsa a film din wato Gabon ta gane.
Inda ake tunanin ita Zarah Diamond itace bakuwar fuskar da zata fito a cikin Shirin a matsayin wadda Adnan Sumaila wato Daushe zai yi wuff da ita.
Kuma bugu da kari shine director film din wato Falalu A Dorayi shine ya wallafa wadannan hotuna a shafinsa. 
To kunga kenan zargin da ake ya tabbata cewa Daushe zai yi wuff da Zarah Diamond ne a cikin shiri Gidan Badamasi mai dogon zango da ake haskawa a Arewa24.


Allah Ya tabbatar mana da dukkan Alkhairi a ko Ina Ameen

Comments