Main menu

Pages

GANYEN KABEWA, AMFANINSA DA IRIN MAGUNGUNAN DA YAKE

 Magungunan da Ganyen kabewa ke magancewa cikin yardan Allah.

Ba wai iya Kabewar ce kadai abin amfani ba, hatta ganyenta ma yana da matukar amfani ga lafiyar mu kwarai da gaske. Sauran Kabilun kasar nan da ma na wasu kasashen Africa sun dade suna amfani da ganyen kabewa wajan yin miya da shi irin yadda muke yin miya da ganyen alayyaho ko ganyen Ugu.


Ganyen kabewa yana tace jini ya raba jini daga gurbacewa cikin yardar Allah.

Ana so masu ciki da masu shayarwa da masu fama da rashin karfi ko kuzarin jiki su rika cin miyar ganyen Kabewa.


Ana so masu matsalar hawan jini da ciwon diabetic, Cancer ( ta Mama ko ta jini) ko HIV su rika amfani da shi wajan matse ganyen (da duk abinda yakamata a matse) sai a rika shan ruwan. Insha ALLAHu akwai fa’ida kwarai da gaske.

Jaririn ganyen wato sabon toho, ne wanda yake fitowa daga sama ake amfani da shi, ba wai manyan ganyen ba wadanda suka dade a jikin kabewar ba


Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Comments