Main menu

Pages

AMFANIN SAIWAR ZOGALE GUDA GOMA SHA DAYA DA BA KOWA YA SANI BA

 Amfanin saiwar Zogale guda goma sha days da ba Kowa ya sani ba.

Kamar yadda kowa ya sani cewa Zogale na da dumbin amfani ga Lafiyar Jiki, to haka ma saiwar Zogalen. Mun tsinto wasu daga cikin Amfanin saiwar Zogalen gasu kamar haka;1- Dattin Mara; A dafa Saiwar Zogale da Tafarnuwa, Asha Sau 2 a Rana Kwana 3,
2- Qatfin Maza; Aci Saiwar Zogale da Namijin Goro,
3- Sanyin Qirji; A ci Saiwar Zogale da Citta,
4- Zafin Fitsari; Adafa Saiwar Zogale da Kanumfari Asha Sau 3 har Kwana uku
5- Ni'imar Maza; A Sha Garin Saiwar Zogale Cukali Daya da madarar Ruwa Gwangwani daya,
6- Sanyi; A dafa Saiwar Zogale da Saiwar Bini da Zugu da Tafarnuwa Kwara Daya asha Sau 2 haiku.

7- Tari; A kwa6a Garin Saiwar Zogale da Zuma Asha Cukali Daya Kullun Har Kwana  bakwai.

8- Ni'imar Mata;  A dafa Saiwar Zogale Adibi Ruwan Rabin Kofi da Dumi Asa Rabin Gwangwani Madara A Sha,

9- Hawan Jini; A Hada Ruwan da Aka dafa Saiwar Zogale da Ruwan da Aka Dafa Ganyen Zogale, Asha Sau uku har Kwana uku.

Yana Saukar da Hawan jini Sosai cikin yardan Allah.
10- Sugar (Diabetes); Cin Garin Saiwar Zogale A Cikin Abinci Yana Saukar da Ciwo Suga Sosai
11- Rage Qiba; Dafa Saiwar Zogale a Dibi Rabin kofi a Matsa Lemun Tsami (Lime) Guda Daya Asha,


Allah Ya bada Lafiya Ya sa a dace

Comments