Main menu

Pages

AMFANIN GARIN CITTA DA YADDA YA KAMATA ANA AMFANI DASHI

 Amfanin Garin Citta da yadda za ana Amfani dashi, don samun waraka daga wasu cutuka

Idan ba ka da garin CITTA a ajiye a gidanka to ya kamata ka siyo cittar sai ka nika ta ta niku tayi laushi sosai sai ka ajiye, domin tana da amfani da dama game da lafiyar mu kamar haka:
1- Idan mace tana fama da matsalar rashin daidaiton al'ada, ko zubar jini ( bleeding) to ta rika amfani da garin citta, za ta samu lafiya DA IZININ ALLAH.
2- Garin Citta yana wanke sikarin da ke cikin jinin mutum da yake haifar da ciwon diabetes DA IZININ ALLAH.
3- Garin citta yana wanke mara da duk wani tarkacen da ke makalewa a marar mutum da IZININ ALLAH.
4- Idan mace ta haihu ko ta yi bari (miscarriage ) to ta rika amfani da garin Citta domin yana wanke mahaifa kuma ya taimaka wajan karawa mahaifar lafiya DA IZININ ALLAH.
5- Idan mutum na fama da sanyin da yake kama kirji ko numfashi kamar Asthma da sauransu, to ya rika amfani da garin citta DA IZININ ALLAH.

Yadda Ake amfani da Garin citta 

Za a nika garin cittar ne ko a daka shi yayi laushi sosai, sai a rika dibar babban Cokali 2 ana zubawa a ruwan zafi kimanin Kofi 1 da kuma zuma ko sikari babban cokali 2 a ciki sai a rika sha safe da dare.


Kuma a rika sanya garin cikin girki idan za'a dafa abinci kamar: Miya, Nama, ko abinci mai dafa-duka.

Insha ALLAHu za a dace... Allah yasa mudace.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 


Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, Shi kadai Ne abin dogara ba maganin ba.

Comments