Main menu

Pages

AMFANIN ADUWA DA MAN ADUWAR GUDA SHA BIYU

 Amfani 12 da aduwa da man ta ke yi a jikin dan adam:


 Bishiyar  Aduwa sanannen abu ne a kasar Hausawa musamman a karkara

Shi dai ‘ya’yan aduwa ana tsotsan sa ko kuma sha

Man shi da ‘ya’yan shi ana amfani dasu wajen magunguna da dama

Bishiyar Aduwa itace ne dake fidda kwallaye masu matukar amfani a jikin mutum. Aduwa ta yi matukar suna a kasar Hausawa musamman a karkara.


Shi dai wannan ‘ya’yan aduwa tsotsansa akeyi ko kuma sha. Bayan sha da ake yi akan tatsi mai daga kwallan Aduwa. Ana kiranta da ‘Desert Date’ da turanci.

Bincike ya nuna cewa tsotson kwallon man dake cikin ‘ya’yan, sannan kuma ita kan ta itacen na da matukar mahimmanci.
Ga amfanin Aduwa a jikin mutum kamar haka:

1. Aduwa na kawar da cutar asma.


2. Mai fama da atini da zawo zai samu sauki idan ya tsotsi Aduwa


3. Aduwa na kawar da tsutsar ciki.


4. Yana maganin ciwon shawara.


5. Aduwa na maganin farfadiya.


6. Man kwallon Aduwa na rage kiba a jiki, idan ana girka abinci da shi.


7. Yana warkar da ciwo a jiki musamman idan ciwon ya zama gyambo.


8. Man Aduwa na maganin sanyin kashi da kuraje.


9. Yana kawar da kumburi.


10. Yana kawar da matsalar yin fitsari da jini.


11. Man Aduwa na gyara fatar mutum da hana saurin tsufa.


12. Yana kuma kawar da ciwon bugawan zuciya.

Comments