Main menu

Pages

YANDA ZAKI GWAJIN CIKI A GIDA CIKIN SAUKI BA TARE DA WATA WAHALA BA

 Hanya Mafi Sauki Tayin Gwajin Ciki A Gida

Wannan hanya ce mafi sauki da zakiyi gwajin don tabbatar da kina da ciki ko babu a gida ta yin amfani da fitsarinki da kuma gishiri.


Abubuwan da zaki nema sune;

- Fitsarinki na farko kafin kici komai da safe da Kuma gishiri.


Yadda zakiyi shine, zaki samu roba wankakkiya kiyi fitsarin ki na farko da safe a ciki, sai ki debo gishiri kadan ki zuba a cikin fitsarin 


Sai ki lura lokacin da kika zuba gishirin cikin fitsarin yayi kumfa ko bai yiba, idan da kika zuba gishirin cikin fitsarin yayi kumfa to kina da ciki, idan kuma bai yi kumfa ba to baki da ciki.


Amma fa abinda ya kamata ku sani shine ba kowane gwajin ciki na fitsari ne yake nuna akwai ko babu ba. Gwajin Jini shine yake da tabbas. Allah Ya bamu sa'a.

Comments