Main menu

Pages

YANDA ZA A MAGANCE ZAZZAFAN TARI DA MURA NA YARA DA MANYA




 Maganin zazzafan Tari da Mura na kananan Yara da Manya.


A lokacin sanyi ko lokacin sauyin yanayi kamar yanzu,  yara/manya suna yawan fama da yawan tari ko mura to Insha Allah ga hanyar magancewa cikin sauki amma a tabbatar tarin na mura ne bana cuta ba.


BANGAREN YARA:


 Jariri Dan Shekara daya Zuwa Shida

Idan jariri ne bai wuce wata daya zuwa shida ba za a samu man tafarnuwa a rika shafa masa a hancinsa da kirjin sa kullum safe da yamma, a kiyaye yi masa wanka da safe ko barin sa iska tana samun sa.




Yaro Dan wata bakwai Zuwa Shekara daya

A samu man shanu a hada da man zaitun a rika shafe masa hancin sa da kirji sau 2 a rana, sannan a rika diga masa man tafarnuwa wanda aka hada da man hulba,kamar digo 5.



 

Yaro Dan Shekara daya Zuwa biyu

Ana samun zuma kamar chokali 5 lemon tsani karami a Raba 4 a matsa rabi akan zumar a rika bashi rabin karamin chokali 1 da safe da yamma..



Yaro daga Shekara uku Zuwa Shida

A samu kajiji, tafarnuwa sassaken marke dai-dai gwargwado, a tafasa a sauke a saka zuma asha sau uku a rana da dumi kamar shayi. 



Bangaren Manya daga Shekara bakwai abinda yayi sama.

- Na farko a samu kajiji, tafarnuwa sassaken marke dai-dai gwargwado, a tafasa a sauke a saka zuma da lemon tsami rabi asha sau uku a rana da dumi kamar shayi. 


- Na biyu ana narka manja original asa suga kadan da lemon tsami rabi asha sau uku a rana. 


- Na uku masu fama da tari da mura ko dattin kirji sakamakon taba ko kura sai a samo:-

1. Ciyawar buruku. 

2. Citta. 

3. Kanumfari. 

4. Lemon tsami. 

6. Zuma. 

A hade number 1 to 3 kowanne garin sa cikin karamin cokali da ruwa karamin kofi 3 a tafasa a sauke a matse lemon tsami mai ruwa babba daya (banda me ulcer) zuma rabin karamin kofi a zuba a flacks ana sha kamar shayi kullum a shanye wannan hadin daga safe zuwa dare har a warke InshaAllah.

Comments