Main menu

Pages

'YAN KANNYWOOD SUN SHA RUWAN MILIYOYIN KUDI DAGA BOLA AHMAD TUNUBU

 Yadda Tunubu yayi was 'yan Kannywood ruwan Nairori da gudummuwar Miliyoyin kudi

Kano – Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya gwangwaje masana’antar Kannywood da gudumawar N50 miliyan domin cigaban masana’antar.

Legit hausa tai rahoton cewa, Tinubu ya bayar da wannan makuden kudaden ne a yayin da ya halarci taro na musamman da ‘yan fim suka hada masa a daren Lahadi a fadar gwamnan jihar Kano.
A yayin jawabi kan manufar taron, Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ya ce:

"Wannan taron na matasan fim ne masu goyon bayan Tinubu. Sun shirya shi a karkashin gidauniyar Kannywood don su nuna yadda karfin goyon bayan da yake da shi a wurin ‘yan fim.
“A saboda Haka a shirye suke domin bashi dukkan goyon baya don ganin ya kai ga nasara.”

A jawabin shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Najeriya, MOPPAN na kasa, Dakota Ahmad Sarari, ya sanar da cewa Kannywood a matsayin babbar masana’antar da ke kawo kudin shiga da aikin yi ga matasa.

Don haka yayi kira ga Tinubu da ya duba yadda masana’antar take idan ya samu cin zabe.


A jawabin tsohon shugaban MOPPAN kuma jarumin fim, Alh Sani Mu’azu, yayi kira ga Tinubu da ya zuba ‘yan masana’antar a cikin yakin neman zabensa saboda masoyan da suke da shi da kuma jama’a.
Yayin mayar da martani, Gwamna Samuel Lalong, shugaban kwamitin yakin neman zaben Tinubu na kasa ya sanar da su cewa daman suna cikin tafiyar dumu-dumu.


Hakazalika, ya sanar da gudumawar naira miliyan hamsin da Tinubu ya bai wa masana’antar domin inganta ta.


Jama’ar da suka halarci muhimmin taron sun hada da dukkan kungiyoyin dake masana’anta

Comments