Main menu

Pages

YADDA AKE SARRAFA KHUSBARA (CORIANDER SEEDS) DON MANCE CUTUKA

 Yadda Ake sarrafa Khusbara domin magance cututtuka daban - daban

Khusbara wato Coriander seeds yana dauke da sinadarai masu matukar mahimmanci ga lafiyar dan adam don haka wasu kasashe irinsu india suka maidashi abincinsu na yau da kullum .


   Kadan daga cikin Amfanin sa

Yana magance dukannin cutar da ta shafi fata irinsu tautau, kefsi, kanzuwa, pimples, kaikaiyin jiki da sauransu.

  Yadda Ake amfani dashi: Sai asamu garin khusbara a kwaba da zuma ashafe jiki dashi bayan minti 15 sai a wanke haka za'a rinkayi har tsawon sati guda.
- Yana magance kurajen baki idan aka tafasashi ana kuskura baki dashi safe da yamma.


- Yana kara yawan gashi da tsawo da sakashi baki idan aka hada garinsa da man gashi ana shafawa agashi sau biyu duk sati.
- Yana narkar da abinci kuma yana bude kafofin jini idan aka jikashi ana shansa kullun da safe kafin a karya.  


- Yana maganin sanyin jiki da mura idan ana barbadawa a abinci mai dumi.
- Yana maganin ciwon suga (diabities) idan aka jikashi da ruwa litre daya ashanye ayini daya ana fara shansa kafin a karya haka bayan an karya har litre dayan ya kare.


- Yana kashe kwayoyin cuta kowani iri (bacteria) sai ayi yajin garinsa ko kuma ahada garinsa da curry arinka cinsa a abinci ko sallad.
- Domin cutukan da suka shafi ido ko yanar ido sai ajika khusbara arinka wanke ido dashi da safe idan an tashi daga bacci da dare kafin a kwanta bacci.


- Domin magance ciwon ciki ko mara na mata a lokacin Al'ada  sai asamu cokali biyu na garin kusbara da sugar(sukari) cokali daya sai a tafasa da ruwa litre daya ya tafasa sosai sai asha da dumi duminsa wallahu ta'ala a'alam.

Comments