Main menu

Pages

MALAM DAURAWA ZAI WUFF DA YARINYAR DA TA CINYE GASAR QUR'ANI TA KASA.

 


Malam Aminu Ibrahim Daurawa Zai angwance da yarinyar da ta ci gasar karatun Qur'ani na Kasa.

Wani labari daya bazama a shafin sada zumunta na zamani musamman ma Instagram da kuma Facebook sun bayyana cewa fitaccen Malamin Addinin nan a Kano Sheikh Aminu Daurawa zai angwance da tsaleliyar budurwa wadda ta lashe gasar Musabakar Al Qur’ani ta kasa kamar yadda Alkaluma suka bayyanawa duniya.Amaryar Malam Aminu Ibrahim DaurawaMalamar ajin ta wallafa a shafin ta na Facebook da Instagram kamar haka:


Ga fa amaryar malam (Guess which malam? Clue Babban malam na kasar Kano, Yana yawan questions and answers)


Kamar yanda aka ce malam yayi halin late comers! Yana zuwa ya doke kowa, wato Malam dai ya cika Jarumi yazo daga baya Kuma ya doke dukkan masu Neman Aurenta. A takaice dai shine zakaran gwajin dafi. Allah Ya sanya alheri. Ya kuma bada zaman Lafiya.


Ga katin Daurin Aure nan kamar yadda wasu suka wallafa a kasan bayanin Malamar AjinComments