Main menu

Pages

IRE - IREN ABINCIN DA KE JANYO MA HANTAR DAN ADAM MATSALA.

 



Kalolin Abinci Guda biyar dake saurin Illata Hantar Dan Adam

Hanta dai wata tsokace mai matukar amfani ce ajikin Dan adam, hanta na taimakawa wajen lalata wasu kwayoyin jini da suka lalace





Ana samun hanta ne a cikin dan adam Hanta dai wata aba ce mai matukar anfani a cikin jikin dan adam ake samu a cikin cikin dan adam. Ko shakka babu hanta mai lafiya kusan dai-dai take da mutum mai lafiya haka zalika hanta marar lafiya ma dai-dai take da mutum marar lafiya. 




Don haka ga wasu jerin kalolin abinci dake janyo ma hanyar Dan Adam matsala. Gasu kamar haka;



1-Abinci mai kitse 

Dukkan dange-dangen abinci matsu kitse na da matukar hadari da lafiyar hantar dan adam. Abincin da ke da kitse yakan ba hanta wahala sosai kasantuwar ita ce ke kula sarrafa dukkan abunda ke shiga cikin dan adam. Yawan cin kitse kan cutar da ita sosai. 





2- Suga:

Kadan daga cikin ayyukan hanta shine sarrafa suga zuwa sinadarin kitse kuma kamar yadda muka karanta a sama, yawan hakan ma kansa yana da lahali ga lafiyar hantar. 





3. Gishiri:

Binchiken masana ya nuna cewa abinci mai gishiri kan yi lahali ga jiki musamman ma dai kasantuwar hanta ita ce ke da alhakin sarrafa sinadarin. Yawan gishiri kan wahalar da hanta ya sanya mata cuta.




4- Giya:

Shan giya ma dai kan taimaka wajen lalata hantar dan adam kasantuwar cewa takan wahalar da hantar wajen sarrafa ta. 





5- Abincin makulashe na gwangwani:

Kasantuwar yawancin wadannan abincin na dauke da gishiri da suga mai tarin yawa, hakan kuma na matukar wahalar da hanta wajen sarrafawa


Dafatan za a kiyaye 


A turawa yan uwa su amfana

Comments