Main menu

Pages

ILLOLI TAKWAS DA KAN SAMU QWALWAR YARA YAYIN JIJJIGASU

 



Matsalar dake faruwa ga kwakwalwar Yara lokacin jijjigasu wajen raino

Daga cikin matsalolin da yara, musamman 'yan ƙasa da shekara biyu ke fuskanta yayin raino akwai matsalar nan ta 'Shaken Baby Syndrome' a turance. Wannan matsala ce da yara ke fuskantar jijjigawa a ƙoƙarin lallashin su yayin da suke kuka ko kuma yayin yi musu wasa. Yara sun fi fuskantar wannan ƙalubale ne musamman yayin da suke hannun masu raino ko kuma iyaye maza.




Jijjiga yara na da gagarumar illa ga ƙwaƙwalwa, wani lokacin ma na iya sanadiya mutuwar yaro.


Kamar yadda aka sani, wuya ne ke ɗauke da kai, kuma tsaiwa ko daidaituwar kai ya dogara ne ga ƙwarin tsokokin wuya. Tsokokin wuyan yara 'yan ƙasa da shekara biyu kuwa basu gama yin ƙwarin da za su iya riƙe kai sosai ba, musamman yayin jijjiga su. Saboda haka, jijjiga su na iya yin lahani ga ƙwaƙwalwarsu, da kuma janyo mummunan rauni ga wuya wanda na iya shafar laka.





Daga cikin matsalolin da ke biyo bayan jijjiga yaro akwai:

1. Ɓallewar jijiyoyin jini a cikin kai.

2. Bugun ƙwaƙwalwa, idan ƙwaƙwalwa ta bugu da ƙoƙon kai daga ciki.

3. Takura ƙwaƙwalwa; yayin da jini ya taru a gefe ko kewayen ƙwaƙwalwa zai takura ko matse ƙwaƙwalwar.

4. Katsewar iskar oxygen zuwa ƙwaƙwalwa, saboda numfashinsu na ɗaukewa yayin jijjiga su.

5. Lahani /rauni ga laka.

6. Karayar ƙoƙon kai idan aka buga kan yaro da bango, kujera, daɓe da suransu yayin jijjiga su, hakan kuma zai iya janyo karaya a ƙoƙon kai.


Akwai buƙatar iyaye da su sake lura saboda wannan matsala ba a gane ta afku a zahiri saboda ƙwaƙwalwa take shafa. Sai dai, yaron da ya fuskanci jijjigawa sosai na iya nuna wasu alamu da zarar an jijjiga shi zuwa awanni shida.


Alamun sun haɗa da:

1. Fita daga hayyaci

2. Amai

3. Suma

4. Ƙin karɓar abinci/abinsha

5. Kakkafewar jiki ko jijjiga irin ta masu farfaɗiya

6. Numfashi ƙasa-ƙasa ko kuma riƙicewar salon numfashi


Ana sa ran warkewar yaron da ya samu wannan matsala ne gwargwadon girman raunin da ya afku a ƙwaƙwalwar.


Matsalolin da ke biyo baya sun haɗa da:

1. Shanyewar ƙwaƙwalwa.

2. Shanyewar ɓarin jiki ko ɓangarorin biyun duka.

3. Dakushewar kaifin ƙwaƙwalwa

4. Farfaɗiya, da sauransu.


Daga ƙarshe, ya kamata iyaye su sake sanya ido don magance matsalar jijjiga yara musamman yayin bayar da su raino. A garzaya asibiti da yaro da zarar ya nuna alamun da aka ambata bayan an jijjiga shi ko buga kansa da wani abu.

To Allah Ya kyauta Ya sa mu gane mu daina jijjiga yaranmu.

Comments