Main menu

Pages

ILLAR DA WUTAR GIRKI KE YI GA MATA MASU YAWAN AMFANI DA ITA

 Ko kunsan yawan amfani da wutar girki tana shafar Lafiyar Mata masu amfani da ita

Dubban mata ne ke kwashe tsawon shekaru na rayuwarsu suna sana’oin da suka ta’allaka da wuta, said ai zafin wutar da kuma hayaki kan shafi kiwon lafiyar wasunsu. To ko akwai mafita a likitance?
Sana’ar suyan kosai da waina ko masa da ta abincin sayarwa, dadaddun sana’oi ne da a ka san mata na yi a kasar Hausa da ma wasu kasashen Afrika.Saidai matan da ke kwashe shekaru suna wadannan sana’oi, su kan yi amfani da magungunan gargajiya ko shaye-shayen wasu abubuwan domin kare kansu ko yin maganin wutar da suke cewa tana damunsu.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce jikin mutum na daukar zafi ne idan zafin jiki ya hadu da na yanayi.


Kuma idan mutum ya kasance a inda zafin yanayi ke karuwa akai-akai, to jikin zai kasa sarrafa zafin zuwa yanayin da jikin zai iya dauka. 
Hukumar ta ce ana samun karuwar al.’umomin da ke fuskantar matsanancin zafi a duniya, lamarin da ta alakanta da sauyin yanayi.


Inda aka samu kimanin mutane miliyan 125 da ke fuskantar matsanancin zafi daga shekarar 2000 zuwa shekarar zuwa shekarar 2016.
Yayin da a shekarar 2015 kadai aka samu karin mutane 175 miliyan da ke fuskantar matsanancin zafin idan aka kwatanta da wasu shekarun da abin ke da dan dama-dama.


Hukumar ta wallafa wannan bayanin ne a kan zafi da yadda hakan ke shafar lafiya, a shafinta na intanet a watan yunin shekarar 2018

Comments