Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANI AKAN INGANCIN SHAN SUPPLEMENT DA SHARADIN SHAN SA

 Cikakken bayani game da shan supplement daga bakin Masana magunguna.A wata fira da akayi da Pharmacist Aisha Ishaq Tukur Kaduna, tayi bayanin inganci ko rashin inganci game da shan supplement.
Lokacin da akai mata tambayar shin ko supplement na da illa ne ganin yadda Matan yanzu suka haukace wajen shansa da yadda Ake tallar sa a ko Ina a online da sauran wurare.
Sai Pharmacist Aisha tace ita baza ta iya cewa Shan supplement Yana da Matsala ba Kai tsaye, ita dai abinda ta sani shine, ko wane irin magani za a Sha to fa a tabbatar an San daga Ina yake Kuma da me aka hada maganin.
Bayan haka Kuma a dinga shansa a bisa ka'ida ba wai a kama maganai ayi tasha babu shawaran likitoci ko pharmacist ba.

Sannan ta kara da cewa duk maganin da zaka Sha to ka tabbatar ka sha shi da ruwa, idan akace Ruwa to Ruwa ko Mai sanyi ko Mai dumi what ever dai tace ai Ruwa is natural don haka ko da ruwan sanyi kasha magani babu wata illah.
Sannan ta Kuma cewa Shan magani da Wani lemo ko tea ko Wani abu ba Ruwa ba yana iya jaza ma mutum wata matsala ba tare da ya sani ba, saboda akwai magunguna da yawa da basa haduwa da wani kalan abinci ko abinsha in dai ba Ruwa ba. Sai abincin ko abinshan suje su hade da Wani maganin da alhalin ba a son su hadu, idan wata matsala ta faru sai ayi zaton daga maganin ne.

Alhalin Kuma ba haka bane. To don haka Mata masu Shan supplement ku San irin maganin da zaku Sha sannan kusan da me aka hada shi meye idan an Sha maganin ba a so aci ko asha don kar ya kawo wata matsala. Sai Kuma shansa bisa ka'ida.

Wadannan sune kadai sharadin da pharmacist Aisha ta fada akan masu Shan supplement. 
Kenan a zato na da hasashe na, shan supplement bashi da wata illah kamar yadda wasu ke Fadi, saboda inda akwai matsala pharmacist Aisha da ta Fadi Kuma da taja kunnen Mata akan ire iren wadannan shaye shayen magungunan supplements da akeyi yanzu da ya zama ruwan dare.
A karshe na yaba da kaifin basira na pharmacist Aisha don kuwa bata tallata ma masu sayar da supplement kasuwa ba bata Kuma kushe ba.


Don haka Mata ayi ta Shan supplement Allah Ya tsaremu daga dukkan sharrin daka iya Zuwa dangane da Shan wadannan magunguna.

Comments