Main menu

Pages

HANYOYI BIYAR DA ZA AYI AMFANI DA ZUMA WAJEN GYARAN JIKI KO FUSKA

 



Hanyoyi Guda biyar da za a bi don gyaran jiki ko fuska da Zuma.


1- Na daya Domin samun Fata mai sheki: Idan kuna son fata mai sheki, to zuma ita ce mafi kyawun sinadarin halitta don ba ku wannan shekin da kuke bukata. Zaku iya hada danyen zuma da ruwan aloe vera. Sa’annan, ku shafa hadin a fuskar ku kafin ku kwanta barci da daddare.




2- Na biyu Domin kawar da Busasshen Leɓe: Zaku iya kawar da busheshen leɓe ta hanyar amfani da zuma. Abu ne mai sauqi, sanya danyen zuma a lebban ku kafin ku kwanta barci! Kuma ku farka da lebe mai taushi da santsi.




3 - Na uku domin kawar da tabo : Shin kuna son share wannan tabon da ke fatar ku? Toh abun da kawai za ku yi shi ne amfani da asalin ɗanyen zuma na halitta a fatar ku. Sai a bar shi da daddare kuma ku ga yadda fuskar ku zata kasance washe gari.




4- Domin kawar da gishirin fuska watto blackheads: Don kawar da gishirin fuska, abin da kawai za ku yi shine cakuda zuma da ruwan lemo, sannan ku shafa a wuraren da abin ya shafa kafin ku kwanta barci.





5- Domin magance Kuraje: Cire kurajen fuska cikin dare daya ta hanyar sanya danyen zuma a wurin da abin ya shafa sannan a rufe da bandeji. Washe gari sai a dauraye fuskan da ruwa.




Karin bayani, shafa Zuma a fuska na da takura sosai balle Kuma ace a kwana da ita, Wanda yaga ba zai iya shafawa ya kwana da ita ba zai iya shafawa kowane lokaci. Amfanin shafa maganin gyaran Fuska a kwana dashi yafi saurin aiki ne.

Comments