Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANI GAME DA SHAN MAGANI KO ALLURAN KIBA DA MATA KEYI

 Cikakken bayani game da Mata masu shan kwayar magani ko yin Alluran Kiba.

A yanzu muna wani lokaci da mata suke yayin shan kwayoyi da allura dake saka su kiba su kumbura su yi jiki sosai
Wannan abune da ya shafi kiwon lafiya, don haka na tambayi Likitoci biyu abokai na, Likita ya fada min cewa tabbas akwai allurai da kwayoyi wanda mata suke amfani dashi domin suyi kiba, har sunayen allura da kwayoyin ya fada min, wato ba kiban Allah da Annabi ba
Akwai kuma kwayoyi da allura da mata ke amfani dashi don hana daukar ciki wato na tsarin iyali, suma suna saka mace tayi kiba, sai dai a wannan zamani ba matan aure kawai suke yin tsarin iyali ba, har da 'yan matan da suke yin karuwanci a gaban iyayensu da kuma shahararrun karuwai da suke zaman kansu
Na taba jin Sheikh Aminu Daurawa yana bada labarin wata dalibar makarantar Sakandare, tayi laifi ne sai Malaminta ya dake ta da bulala a dantsen hannunta, nan take jini ya fara kwarara, da aka kaita asibiti likita na dubawa sai aka tarar ta saka robar implant a dantsen hannunta na tsarin iyali dake hana daukar ciki ba tare da sanin iyayenta ba, gurin ne Malamin ya daka a rashin sani
Ni ganau ne ba jiyau ba, domin shekara 6 da suka wuce mun taba gwada irin wannan tsari da matata, na ga ya kumbura min Matana tayi kiba sosai, kuma duk wani mai iyali ya san haka na faruwa musamman idan planning din ya karbi mace
Sannan akwai kwayoyin da mata masu cutar HIV suke sha, shima yana kara musu kiba suyi bul-bul har da sheki, zaka dauka sun fi wadanda basu da kibar lafiya
Likita yace min, kwaya ko allura da mata suke sha domin su yi kiba yana da matukar illa, kuma yana haddasa cutar kansa mai wuyar magani, yace min, duk abinda ba Allah ne ya halicci mutum da shi ba, sai dan adam ya kirki wani magani daga cikin sinadarai domin a canza halittar Allah to yana da illa ga lafiya
Musamman allura da kwayoyin da aka samar domin kawai su sa mace tayi kiba, to ba wai kawai ordinary kiba sukeyi ba, rubar da su sinadaren yakeyi sai su kumbura, su a zatonsu kiba sukayi, alhali gyambo ne, sun rube ne ta ciki suka kumbura, kuma babu wacce zatayi wannan ta wanye lafiya, kuma tafi kowace irin mace possibility na kamuwa da cutar kansa
Samari da tuzurai suna ganin mata masu kiba sunfi sirara dadi, to ni a fahimtata ra'ayi ne wannan, a matsayina na magidanci na fahimci mace kowa da irin halittar ta, wannan babi ne da bana so na budeshi, saboda akwai yara da bai kamata su sani a yanzu ba
Wannan yana daga cikin dalilin da yasa wasu mata suka koma yin allurar kiba domin su burge mazaje, su kuma mazan da basu san sirrin ba sun dauka cewa lallai mai kiba tafi gamsarwa, mace ko ya take, matukar ka kula da ita musamman da abubuwan da take ci zaka samu abinda kake so ko da ta kai allura siranta
Daga karshe ina baki shawara ya ke mai yin allura don kiyi kiba, ki sani yana da illa, idan cutar kansa ta kamaki maza gudunki zasuyi, don haka kar a gurin gyaran gira a rasa ido, ki tsaya a yadda Allah Ya ajiyeki, kuma ki sani akwai na mijin da sam a rayuwarsa bai son mace mai kiba

Allah Ya sa mu dace

Comments