Main menu

Pages

AMFANIN MISKI GA MACE DA YADDA YA KAMATA TAYI AMFANI DASHI

 
Amfanin Miski ga Mace da yadda ya kamata tayi amfani dashi.

Shidai miski turarene me Kamshi, kamshin kuma maisa nishadi da annashuwa.

Yanada kyau kwarai da gaske ace a matsayin ki na mace koda yaushe yakasance kina da miski a dakinki domin anaso koyaushe kirinka amfani dashi.

Mun riga mun sani shi kamshi abune dayake kara dankon soyayya kuma yake dawwamar da ita, sannan miski yana dauke da sinadarai da dama da suke bawa farjin mace kariya daga cututtuka, saboda haka anaso kullum mace tarinka amfani dashi.

Kalolin Miski guda uku 3 ne gasu kamar haka:.

- Akwai Fari mai kamar madara mai kauri:

shi wannan ba a sashi acikin farji saboda adaskare yake bai fiya narkewa ba, sai dai ashafashi daga wajen farji.

- Akwai fari kal kamar ruwa kamshinsa kusan dayane da mekaurin sai dai shi bashida kauri, to shi za a iya "inserting"(matsi)dashi tabbas yana taimakawa har a6angaren auratayya kuma duk sanda mijinki yaji wannan kamshin ko bakwa tare to zai tunaki Zaiyi sauri sauri ya dawo gida kinga miski yayi amfani kenan.
- Akwai jan miski wannan masu fama da matsalan aljanu suke shafashi domin yana fatattakar aljanu da iznin ALLAH

Abinda nasani dai idan me aljanu tana shafashi idan anriga ammata rukiyya to suna rabuwa da ita cikin yddar Allah

Amma idan ba ayiba to zakaga batasan kamshinsa baza tayi amfani dashiba


Shi ana shafashine aduk jiki da ga6ar da tafiyiwa me fama da aljanun ciwo

Kunsan fa miski asali yadauko yanada kyau kiyi taka tsantsan gurin amfani dashi domin bawai kawai dangwala zakiyi da yatsanki kisakaba a'a,


Zaki nemi ruwan dumine bamai zafi sosai ba kije ki kama ruwa dashi ki wanke gurin sosai, sannan kisami handkerchief mekyau ki goge ko da tissue, daganan saiki sami "cotton bud" wato abin sosa kunne

:

Sai ki dangwalo dashi sannan kiturashi agabanki kidan matse kafarki sai kicire ki yar.

to wallahi ko fant dinki kika cire kamshi zakiji yana yi.


Babu kunya cikin neman ilmi musamman ilmin addini babban abun kunya ace mijinki zai kusanceki kuma yaji farjinki yana wari haba wannan ai ba aji.


Zaki iya dafa ganyen magarya inya huce kizuba miskin kina kama ruwa dashi.


Sannan anaso duk sanda zaki saka pant dinki to ki diga miskin akai duk wasu kwayoyin cuta zasu mutu da yardar Allah.


Ana kuma shafa miski ajiki ana kuma hadashi acikin Humra yana kuma taimakawa macen data haihu kwarai da gaske.

Comments