Main menu

Pages

AMFANIN DABINO (AJWA) GUDA GOMA GA LAFIYAR DAN ADAM

 



Amfanin Dabino (Ajwa) guda goma ga Lafiyar Dan Adam


Bayan amfanin da wannan dabino yakeyi wajen warware SIHIRI, kanbun baka dakuma korar jinnu ajikin dan Adam, yanada Wasu amfani nadaban ajikin dan Adam wanda zan kawo muku goma daga ciki kamar haka:




1- Yana boosting immune system; wato yana ƙara karfafa garkuwan jikin dan Adam Saboda Wasu sinadarai, ma'adanai da vitamins da yake kunshe dashi, don haka yin amfani dashi kariyace daga kamuwa da cututtuka.





2- KARIYA DAGA CUTAR CANCER:- Dabinon Ajwa yanada tasiri sosai wajen samun Kariya daga cutar daji wato CANCER da sauran cututtuka na zamani saboda wasu Ma'adinai da yake kunshe dashi Mai faɗa da cututtuka, Sannan Yana taimakawa wajen rage radadin ciwo, Wato itama pain reliever ce.





3- SAUKIN NARKEWAR ABINCI:- Dabinon Ajwa yanada tasiri sosai wajen saukin narkewar abinci saboda sinadarai da yake kunshe dashi wanda yake kawo sauƙin digestion na abinci tareda magance Constipation wato rashin samun bahaya akai akai.






4- YANA MAGANCE KARANCIN JINI :- Amfanida Dabinon Ajwa yana taimakawa masu ƙarancin jini saboda karancin sinadarin IRON ajikinsu, domin Dabinon Yana kunshe da sinadarin IRON mai yawa wanda jikin mutum yake buƙata domin samarda Red blood cells daily.






5- YANA MAGANCE MATSALAN KASHI:- Dabinon Ajwa yana kunshe da Vitamins da Ma'adanai Masu yawa Kamar irinsu PHOSPHORUS dakuma CALCIUM wanda suke taimakawa Wajen karfafa Kashi tareda samun Kariya daga matsalan raunin Kashi.





6- SAUKIN NAKUDA-: Dabinon Ajwa yanada tasiri sosai wajen karawa jinjiri lafiya, Kawo saukin nakuda tareda saukaka zafin haifuwan, saboda tasirinsa wajen buɗe bakin mahaifa lokacin nakuda.






7- RUWAN NONO:- Dabinon Ajwa yana taimakawa mata masu shayarwa Wajen samarda taceccen ruwan nono wanda jinjiri zaisha tareda karfafa masa garkuwan jiki.






8- INGANTA LAFIYARTA ƘWAƘWALWA:- Dabinon Ajwa yana taimakawa Wajen inganta lafiyar ƙwaƙwalwa tareda karawa yara da manya basira kuma yana magance matsalan yawan mantuwa.







9- LAFIYAR ZUCIYA-: Yana daga cikin abinda Dabinon Ajwa ya shahara wajen magancewa, matsalolin zuciya, yana daidaita bugun jini acikin zuciya, yana rage kitse Mai cutarwa ajiki wato cholesterol tareda samun Kariya daga Heart attack.





10- LAFIYAR IDO:- Dabinon Ajwa yana taimakawa sosai wajen karfafa lafiyar ido tareda magance matsalan gani dishi dishi, makantan dare, yanar ido, sannan yana karawa ido kaifin hangan nesa da gane ƙananan rubutu.

Comments