Main menu

Pages

AMFANIN ABARBA GUDA GOMA SHA DAYA GA LAFIYAR DAN ADAM.

 Amfanin Abarba guda shadaya (11) ga Lafiyar Dan Adam

Abarba na daya daga cikin yayan itatuwa masu amfani a jikin dan adam. 


Abarba na da matukar amfani a jikin dan adam saboda tana dauke da muhimman abubuwa; fibres, menirals, vitamins, Nutrient da kuma Anti Oxidant. 

Kaman yadda Legit.ng ta ruwaito wadannan sinadarai dai dake a cikin abarbar na da matukar amfani ga rayuwar dan adam, sannan takan kare jiki daga cututtuka. 
 1. Tana dauke da sinadarin magnees da calcium wanda ke kara karfin kashi.


2. Tana dauke da anti oxidant wanda ke kara ma jiki lafiya da kare jiki daga saurin tsufa. 


3. Tana maganin mura da sanyin kirji. 


4. Tana kara ma garkuwar jiki lafiya da kare shi daga cututtuka. 


5. Tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage cholesterol a jiki. 


6. Tana kara lafiyar dasashi da kare hakora. 


7. Tana saukaka yawan laulayin ciki, da yawan amai da yawan tashin zuciya. 


8. Tana maganin tsutsar ciki. 


9. Tana kara ma idanu lafiya 


10. Tana kara lafiyar ciki da saukaka bahaya 


11. Tana maganin kumburi da maganin ciwon gababuwa.


 Da fatan zamu rinka shan abarba akai akai.

Comments